Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da ƙara kuɗin harajin shigo da man fetur da dizal kashi 15.
Wannan na cikin wata wasiƙa da aka rubuta a ranar 21 ga watan Oktoba, 2025, wacce Damilotun Aderemi, sakataren shugaban ƙasa na musamman, ya sanya wa hannu.
An tura wasiƙar zuwa Hukumar Tattara Haraji ta Ƙasa (FIRS) da kuma Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur ta Ƙasa (NMDPRA).
A cewar wasiƙar, wannan mataki ya biyo bayan buƙatar da FIRS ta gabatar don saka harajin kashi 15 a cikin jimillar kuɗin shigo da mai, wanda ya haɗa da kuɗin kaya, inshora, da sufuri (CIF).
Wannan mataki na nufin daidaita farashin shigo da mai duba da yanayin da tattalin arziƙin Nijeriya ke ciki a yanzu.
Masana sun bayyana cewa wannan sabon haraji zai iya sa wa farashin mai ya tashi.
Gwamnati ta ce wannan mataki na daga cikin ƙoƙarinta na ƙara samun kuɗaɗen shiga da rage yawan kashe kuɗi wajen shigo da man fetur daga ƙasashen waje.














