Ƙungiyar Injiniyoyi ta Kasa NSE da Hukumar kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Kasa NPA, sun kaulla hadaka domin kara bunkasa tattalin arziki na teku.
Shugabar kungiyar ta NSE Madam Margaret Oguntala ta bayyana haka a yayin ziyarar aiki da ta kai ga Shugaban Hukumar ta NPA Dakta Abubakar Dantsoho.
- Xi Jinping Ya Halarci Kwarya-Kwaryan Taron Shugabannin APEC Na 32 Tare Da Gabatar Da Jawabi
- Jam’iyyar NNPP A Kaduna Ta Ƙaryata Batun Tsige Shugabanta
Madam Margaret ta sanar da cewa, injiniyoyi na taka muhimmiyar rawa a bangaren habaka tattalin arziki na teku
Ta kuma yi amfani da ziyarar wajen gayyatar shugaban hukumar ta NPA da kuma tawagarsa, domin su halarci taron kungiyar kasa da kasa za ta gudanar a watan Disambar wannan shekarar ta 2025.
Take taron shi ne, “Fasahar da fannin Injiya ke bayarwa wajen kara habaka tattalin arzikin teku”.
Oguntala ta bayyana cewa, ana sa ran babban ministan ma’aiktar bunkasa tattalin arziki na teku Mista Adegboyega Oyetola, zai halarci taron, wanda aka tsara za a gudanar a watan Disambar wannan shekarar a garin Ibadan.
Ta bukaci hukumar ta Hukumar kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Kasa NPA, da ta yi hadaka da kungiyar domin gudanar da taron wanda ta sanar da cewa, Shugaban Hukumar ta NPA Dakta Abubakar Dantsoho ne, zai kasance babban mai gabatar da jawabi, a wajen taron kungiyar.
Kazalika, ta yi kira ga Hukumar ta NPA, da ta dauki nauyin manyan kasidun da za a gabatar da wajen taron tare da samar da ilimi kan batun da ya shafi fannin na bunkasa tattalin arziki na teku.
Shugabar ta kuma bai wa hukumar ta NPA damar da ta yi bajin koli a yayin gudnar da taron, inda kuma ta sanar wa da hukumar ta NPA cewa, ta zabo wasu daga cikin injiniyoyin NPA da ta sanya a cikin kwamtin shiye-shiyen gudanar da taron.
Ta kuma shedawa Dantsoho cewa, wasu masu masana’antu da wasu daga bangaren gwamnati da kuma wasu daga bangaren manyan makarantun kasar nan, na da burin yin hadaka da hukumar ta NPA.
“Mun sa irin kokarin da shugaban hukumar ta NPA key i, musaman wajen kara bunkasa tattalin azrikin da ke a fannin ayyukan Tashoshin Jitagen Ruwan kasar” .
“Muna sane da cewa, ba za mu iya gudanar da gagarumin atron namu, matukar ba mu samu guduanmwar da za ku iya bamu ba, domin shirya taron a acikin nasara, musamman duba da irin gudunmawar da za ku iya bayarwa,” Inji ta.
“Ba wai muna neman hukumar ta dauki nauyin mu bane, muna kawai bukatar yin hadaka da hukumar ta NPA ne , musamman duba da irin gawaurtaccen taron da muke yin yi,” A cewar shugabar.
“Fannin na bunkasa tattalin arzikin teku, abu ne da yake ci gaba da kara tumbatsa kuma abu ne, da ke da makoma mai kyau, haka fannin ne, da har yanzu, mutane ba su gama fahimtarsa ba,” Inji ta.
Ta kara da cewa, idan aka ba za daukacin bangarorin injiniyoyin zuwa rassa guda 93 da ake da su a kasar nan da kuma sauran wadanda suke a kasar waje, hakan zai kara taimaka wa, wajen kara bunkasa kasar nan.
Shugabar ta kuma bijro da batun shigar wadanda suka samu shedar kammala karatun injiniya wadanda suka samu horo daga gun kwararrun injiniyoyi suke kuma yin aiki a hukumar ta NPA.
Ta kara da cewa, bisa matakan bin ka’ida da bangaren gudanar da mulki da kungiyar ta dauka su ne, na tabbatar da duk wanda ya karaci ilimin injiniya dole ne ya kasance ya kai mataki na goma
A na sa jawabin shugaban hukumar ta NPA Dakta Abubakar Dantsoho ya sanar da cewa, kashi 70 zuwa 80 na ma’ikatan da ke aiki a hukumar ta NPA injiniyoyi ne.
Dantsoho ya kuma bai wa shugabar kungiyar tabbacin cewa, za ta yi hadaka da kungiyar ta NSE, musamman domin a kara ciyar da kasar nan gaba, inda ya buga misali da sauran kasashen duniya da suka yi hadaka da kungiyoyin injiniyoyi wanda hakan ya ba su damar samun nasara, musamam ta hanyar yin hadaka.
Shugaban ya sanar da cewa, idan aka yi hadakar da hukum














