Tsohon shugaban babbar kasuwar mile12 intanashinal maket a Legas Alhaji Isa Mohammed Mai shinkafa kuma shugaban kungiyar Dattawan kasuwar ta mile12 dake cikin birnin Legas ya bayyana cewar hakika a halin yanzu al ummar hausawan kasuwar mile12 intanashinal maket da sauran kabilu daban daban mazauna cikin kasuwar a Legas suna kara samun hadin kawunan junan su a Legas da kewayan ta gaba daya Alhaji Isa Mohammed Mai shinkafa wan da ya tabbatar da hakan a gidan sa dake cikin birnin kano alokacin da yake tabbatar ma Jaridar LEADASHIP HAUSA gaskiyar wannan al’amari na halin zaman takewar al ummar hausawa dana sauran kabilu mazauna yankin na Legas gaba daya jim kadan bayan da ya kammala karbar bakuncin dumbin al’ummar Hausawa dana Yarabawa wadanda suka fito daga sassa daban daban na jihohin kasarnan suka zo Kano domin taya shi murnar gabatar da daurin auran ‘ya’yansa guda uku Amira Isa Mohammed da Angon ta Shamsuddini Mai Kudi Kiru da Rabi’atu Isa Mohammed da Angon ta Idiris Abba da kuma Maryam Isa Mohammed da Angon ta Muntari.
Taron daurin auran wanda ya gudana a masallacin Jumma’a na Iya’ussunnah da ke unguwar Gwambaja a cikin birnin Kanan Dabo a ranar Jumma’an nan ta makon jiya daya gabata kadan daga cikin manyan baki a wajan taron daurin auran sun hada da Babban Shugaban kasuwar mile 12 intanashinal maket a Legas Alhaji Shehu Usman Samfam da babban sakataren kasuwar Alhaji Balarabe Idiris da tsohon shugaban kasuwar Alhaji Haruna Mohammed Tamarke sauran sun hada da wadansu daga cikin Iyayan kasuwar wadanda suka hada da Alhaji Habu Faki Garkuwan Faki da Alhaji Abdulwahab Tsoho Babangida da Alhaji Abdullahi burama da sauran shuwagaban nin bangarorin kasuwar ta mile12 shugaban kasuwar Yan doya a mile12 Alhaji Mohammadu Dan Damma Yabo da Tsohon Kwamishinan ‘Yansanda Alhaji Abdullahi Yuguda Tsanyawa ta Jihar Kano da sauran manyan bakin da suka fito daga sassa daban-daban na jihohin Nijeriya Yarabawa da sauran wadansu kabilu daban-daban na kasar nan inda Alhaji Isa Mohammed ya nuna farin cikin sa karara a game da ganin dumbin al’ummar da suka zo taya shi murnar gabatar da wannan al’amari tare da fatan alheri na komawar su gidajen su lafiya.