Kasar Jamus ta sanar da matakan da take dauka domin rage makamashin da ake amfani da shi bayan fari da tsananin zafi da annobar Korona da kuma fadan Ukraine sun haifar da matsalar makamashi a duniya.
Sai dai karuwar matsalar makamashi ta taba ko’ina a duniya, inda Jamus ba ita ce kasa kadai da ta bullo da matakai domin tinkarar hakan.
- Muna Zargin Masallatai Da Coci-coci Da Hannu A Satar Mai –Kyari
- Kasar Sin Na Adawa Da Matakin Amurka Na Keta Ka’idojin Fitar Da Kayayyaki
 Ga wasu hanyoyi bakwai da gwamnatoci suke dauka domin dakile matsalar ta makamashi. Nahiyar Turai na fuskantar matsalar makamashi da ba ta taba gani ba, bayan da Rasha da rage yawan gas din da take fitarwa ta bututun Nord Stream 1.
Hakan ne ya sa dakile matsalar matsalar makamashi ta zamo babban abu da gwamnatoci a Turai din suka sa gaba.
Rage abubuwa masu zafi da kuma na’urar bayar da sanyi
Tarayyar Turai ta dauki matakin rage amfani da gas da kashi 15 lokacin hunturu da kuma tabbatar da cewa cibiyoyin adana albarkatun gas sun cika zuwa kashi 80 kafin nan da 1 ga watan Nuwamba.
Kasashen Jamus da Faransa da Sifaniya na bullo da matakai da suka takaita amfani da abubuwa masu zafi a wuraren jama’a zuwa Celsius 19 lokacin hunturu.
Su ma Faransa da Sifaniya sun saka irin wannan mataki ga nau’rorin bayar sanyi a gine-gine lokacin bazara zuwa Celsius 26 da 27C. Haka nan ma, shaguna masu nau’rorin bayar da sanyi a Faransa za su rika rufe kofofinsu ko kuma a ci tararsu ta Yuro 750.
“Matakai masu sauki kamar rage abubuwan zafi zuwa ma’auni kadan a Turai za su rage yawan albarkatun gas da bututun Nord Stream 1 ke samar da shi a lokacin hunturu,’’ a cewar kungiyar makamashi ta kasa da kasa.
Rufe fitilun wuta
Jamus ta ce ba za a kunna wuta da daddare ba daga yanzu a gine[1]ginen jama’a ko wuraren tarihi, yayin a Sifaniya kuma za a rika kashe wuta a shaguna da misalin 10 na dare. Faransa na da yakinin cewa matakai da ta bijiro da su za su taimaka wajen rage makamashi da ake amfani da shi da kashi 10.
Kasar bata dogara da gas din da Rasha ke samar wa ba kamar makwabciyarta Jamus saboda kashi 42 na wutar lantarkinta na zuwa ne daga tashar Nukiliya.
Sai dai tsananin zafi da fari ya shafi nau’rorin bayar da sanyi a cibiyoyin nukiliya da dama wanda ya tilasta su rage yawan hasken da suke bayar wa.
Samun ruwan sama
China na fuskantar irin wannan matsalar ta makamashi. Yayin da mai da gas din da take samu daga Rasha ya gamu da cikas bayan afkuwatr fada da Ukraine, fari da kuma tsananin zafi sun yi matukar shafar su.
Wannan ya sanya koguna bushewa wadda kuma ya shafi bangaren bayar da hasken lantarki.
A lardin Sichuan, da ke samun kashi 80 na wutan lantarki daga madatsar ruwa, hukumomi sun tilastawa masana’antu rufewa na tsawon kwanaki shida domin rage wutar da ake amfani da ita, inda aka bai wa ofisoshi da kuma shaguna umarnin rufe wuta da kuma nau’rorin bayar da sanyi. Jihohi makwabta kamar Chongking su ma sun dauki irin wannan mataki.
Ministan aikin gona na kasar ya sanar da matakan ‘samar da gajimare’, inda ake sake sinadarai zuwa cikin gajimare domin samun ruwan sama, sai dai ba a sanar da wajen da za a yi hakan ba.
Rage lokutan aiki
Ita ma Pakistan, ta bullo da hanyoyin zamani domin rage makamashin da ake amfani da ita.
A watan Yunin wannan shekara, kasar ta sanar da cewa za ta rage kwanakin aiki a ofisoshin gwamnati daga shida zuwa biyar – wanda kuma ya juyawa matakin baya da aka sanar makon farko a baya, lokacin da sabuwar gwamnati ta karbi mulki a Islamabad da yin alkawarin kara inganta aikin gwamnati.
Makonni kadan daga baya, yanayi ya kai maki 50 na ma’aunin Celsius a Pakistan, wadda hakan ya kawo matsi ga babban layin samar da wutan lantarki a kasar.
Matsalar tsadar makamashi da ake kara fuskanta a duniya, ya sanya abubuwa tabarbarewa, inda a yanzu gwamnatoci ke duba matakan ganin ma’aikatanta sun yi aiki daga gida a ranakun Juma’a.
Rufe makarantu
Kasar Bangladesh ma na daukar irin wannan mataki, inda za a rufe makarantu na karin kwana daya a cikin mako, inda yanzu ranakun Asabar da Juma’a za su kasance na hutu.
An kuma rage sa’a daya ta aiki na ma’aikatan gwamnati a kwana guda daya.
Bangladesh ta dogara da shigo mata da iskar gas, wadda kuma na daya daga cikin nau’ukan mai mafi tsada.
Wannan kuma na nufin za ta yi gogayya da kasashe masu karfin tattalin arziki a Turai kafin samun gas dinta.
Makamin nukiliya
A wasu wurare, karuwar matsalar makamashi ta janyo koma baya na burbushin halittu.
Yawan gawayi da Indiya ke shigo da shi ya matakin sama a watan Yuni, duk da cewa gwamnati ta dauki matakai a baya na rage gawayi da take shigo da shi kasar. Amma kasashe na duba wasu hanyoyi na daban.
Bayan shekara 11 da aka samu bala’in cibiyar nukiliyar Japan ta Fukushima, kasar na duba yiwuwar samar da wata sabuwar cibiyar nukiliya.
Hasken rana
Matsalar ta makamashi za ta iya zama abu da za a iya sabuntawa. Faransa na shirin kara karfi wajen samar da makamashi.
Kasashe kamar Afirka ta Kudu da China na karfafawa ‘yan kasuwa da kuma daidaikun mutane zuba jari a bangaren nau’rorin samar da hasken rana, da bullo da matakai da kuma farashi da zai bar mutane sayar da makamashin wuta zuwa ga babbar layin samar da wutan lantarki a kasar.