Gwamnatin Bola Tinubu ta yaba wa tsohon gwamnan jihar Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso, saboda mayar da martani da ya yi wa shugaban Amurka Donald Trump a fili kan kalaman da ya yi na cewa “Amurka na shirin kutse a Nijeriya.”
Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga, ya bayyana matsayin da Kwankwaso ya dauka a matsayin “kishin kasa”, yana mai kira ga sauran abokan hamayya da su ajiye siyasa a gefe su kare ‘yancin Nijeriya daga barazanar wasu daga “ƙetare.”
- NARD Ta Yi Fatali Da Iƙirarin Gwamnatin Tarayya Na Ba Ta ₦43bn, Kuma Yajin Aiki Na Nan
 - Gumi Ya Nemi Nijeriya Ta Katse Hulɗa Da Amurka Idan Trump Bai Janye Barazanar Sa Ba
 
“Muna godiya ga Sanata Kwankwaso kan kishin kasa. Wannan lokaci ne da ya dace dukkanin shugabannin siyasa, a faɗin jam’iyyu, su hada kai wajen goyon bayan kasarmu su yi magana a matsayin masu kishin kasa,” in ji Onanuga
Kwankwaso, wanda shi ne dan takarar shugaban kasa na NNPP a zaben 2023, ya fitar da wata sanarwa mai karfi yana gargadin cewa, kalaman Trump na iya kara ruruta wutar rikicin addini da kuma kara ta’azzara rashin tsaro a kasar.
A shafinsa na X, tsohon gwamnan ya yi Allah-wadai da matakin Trump na ayyana Nijeriya a matsayin “kasar da ke da matukar damuwa,” wanda kuma ya yi zargin ikirarin “kisan kare dangi ga Kiristoci.”
Kwankwaso, ya yi kira ga Amurka da ta taimaka wa Nijeriya da tallafin fasaha da leƙen asiri maimakon barazana, sannan ya shawarci Gwamnatin Tarayya da ta zurfafa hulɗar diflomasiyya ta hanyar naɗa wakilai na musamman domin tattaunawa.
“Ga ‘yan uwana ‘yan ƙasa, wannan muhimmin lokaci ne da ya kamata mu jaddada haɗin kai maimakon rarrabuwar kawuna. Allah ya albarkaci Nijeriya,” in ji Kwankwaso.
			




							








