Kungiyar Likitan Gwamnati Masu Koyon Aiki (NARD) ta zargi Gwamnatin Tarayya da yaɗa bayanan da ba gaskiya ba game da halin da ake ciki kan walwalar likitoci da sauye-sauyen da ake iƙirarin ana yi a fannin lafiya.
A wata sanarwa da Shugaban NARD, Dr. Mohammad Suleiman, tare da Sakataren Janar, Dr. Shuaibu Ibrahim, da Sakataren Yaɗa Labarai, Dr. Abdulmajid Ibrahim suka sanya hannu a ranar Litinin, ƙungiyar ta bayyana cewa bayanan da ma’aikatar lafiya ta fitar “ƙirƙirarran labari ne wanda ba gaskiya ba,” yayin da asibitoci na gwamnati ke ci gaba da durƙushewa saboda rashin kulawa da alƙawurran gwamnati.
- Tawagar Likitocin Sin Ta Samar Da Tallafin Jinya Ga Kananan Yara Kyauta A Togo
 - Likitocin Sin Dake Aikin Agajin Kiwon Lafiya A Nijar Sun Gudanar Da Tiyatar ALT A Karon Farko A Yammacin Afirka
 
Ƙungiyar ta soki sanarwar da Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya ta fitar a ranar 31 ga Oktoba, inda ta bayyana cewa an yi nufin ruɗar da jama’a ne. NARD ta roƙi Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya binciki gaskiyar lamuran da kansa, maimakon dogaro da rahotannin da aka ƙawata. Ta ce akwai buƙatun su 19 da ba a cika ba, ciki har da biyan bashin albashi da alawus-alawus, da ƙarin kashi 25/35 cikin 100 na CONMESS, da sauran haƙƙoƙi da suka daɗe sama da shekaru biyar ba a biya ba.
Ƙungiyar ta ƙaryata iƙirarin cewa gwamnati ta saki biliyan ₦30 biliyan domin biyan bashin da aka tarawa likitoci, tana mai cewa mafi yawan mambobinta ba su ga ko sisi ba. NARD ta kuma soki tsarin IPPIS, tana cewa shi ne ke haifar da matsalolin ragin albashi da jinkirin biyan kuɗi, tare da kiran a samar da sabuwar hanya ta musamman ta ma’aikatan lafiya.
Haka kuma, ta yi watsi da iƙirarin cewa an ɗauki sabbin ma’aikatan lafiya dubu 20, tana mai cewa adadin likitocin gwamnati ya ragu daga 16,000 zuwa kimanin 9,000 cikin shekaru goma saboda rashin walwala da haɗarin aiki.
Ko da yake ƙungiyar ta yaba da sakin biliyan ₦10.6 ga asusun gidauniyar likitoci masu neman ƙwarewa (Medical Residency Training Fund) (MRTF) na 2025, ta ce biyan ya kamata ya zama na yau da kullum, a buɗe, kuma ya dace da hauhawar farashi.
NARD ta kuma yi tir da dawo da wasu daga cikin likitocin da aka kora a Asibitin Koyarwa na Lokoja (FTH Lokoja), tana mai cewa dole ne a dawo da dukkan su ba tare da sharaɗi ba. Sauran matsalolin da ta jero sun haɗa da bashin albashi da ba a biya ba a BSUTH, da FMC Owo, da OAUTHC Ile-Ife, rashin aiwatar da tsarin one-for-one replacement, da kuma matsalar amfani da likitoci ƴan kwangila a asibitoci da dama.
NARD ta jaddada cewa tana shirye ta ci gaba da tattaunawa, amma ta ce yajin aikin da ake yi yanzu ba domin cutar da ƴan Nijeriya ba ne, sai domin ceto tsarin lafiya da ke gab da rugujewa. “Yaƙinmu ba na neman kuɗi kawai ba ne, sai na tsira da mutunci, da tsaro, da rayuwa cikin aminci,” in ji sanarwar.
			




							








