Kwamitin da ke lura da harkokin manyan makarantu na kasar nan, ya sanar da cewa, akwai bukatar a kara haraji a kan makaratun daga kashi 2.5 zuwa kasha 3 a cikin dari.
A cewar kwamitin, hakan zai kara taimaka wa don manayan makarantun su samu damar gudanar da binciken da za su samar da ci gaba a daukacin fadin kasar.
- Dan Takarar Gwamnan Jihar Ogun Na PRP Bamgbose Ya Mutu , Yana Da Shekara 54
- Dattijo Mai Shekara 74 Ya Yi Aurensa Na Farko A Lakwaja
Kwamtin ya sanar da wannnan bukatar ne, a yayin da ya kai ziyara aiki a gudauniyar bunkasa ilimi ta (TETFund) domin tabbatar da yadda aka kashe kudadedn da aka kebe a cikin kasafin kudi na shekarar 2021 zuwa shekarar 2022.
Sanata Ahmed Babba Kaita, wanda ya jagoranci kwamitin a lokacin ziyara ya ce, fannonin ilimin boko da na kiwon lafiya, fannoni ne manya da ke samar da ci gaba saboda hakan, akwai matukar bukatar a sake sabunta biyan harajin na ilomin.
A na sa jawabin tunda farko, Babban Sakataren TETFund, Sonny Echono, ya bayyana cewa, a shekarar 2021 hukumar ta rabar da naira biliyan 213 ga manyan makaratun kasar har da kudin somin tabi ga sabbin manyan makarantun da aka kirkiro a kasar.