ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, June 4, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Cika Shekara 20 Kan Karaga: Kyakkyawan Shugabancin Mai Martaba Sarkin Hadeja, Dakta Adamu Abubakar Maje

by Mika'il Tsoho
4 years ago
Shekara 20

Ranar 14 ga watan Satumba na kowacce shekara ta kasance wata rana ta musamman ga kafatanin al’ummar Masarautar Hadeja, sakamakon a ranar ne da Mai Martaba Sarkin Hadeja Dakta Adamu Abubakar Maje yake cika shekara 20 a kan karagar mulki a matsayin Sarkin Hadeja (a cikin jerin sarakunan Fulani) na 16 a Masarautar.

Mai Martaba Sarkin Hadeja kuma shugaban majalisar Sarakunan Jihar Jigawa, wadda duk duniya ta yi masa shaida wajen hidimta wa addini da al’ummarsa musamman masu karamin karfi, mata da kananan yara da marayu, ya kasance Sarki Mai ilimin addini da na zamani.

  • Wani Abun Fashewa Ya Tarwatse A Wani Masallaci Ya Kashe Akalla Mutane 18 A Afganistan
  • Mene Ne Hukuncin Aske Gemu?

Haka kuma cikin shekara ashirin da Sarkin ya share kan karagar mulkin Masarautar, an sami gwaggwaban ci gaba a fannonin rayuwa a yankin, wadda hakan ya sanya Masarautar ta Hadeja ta zarce sa a akowanne fanni na rayuwa.

ADVERTISEMENT

Masarautar Hadeja ta kasance daya daga cikin masarautu biyar masu dumbin tarihi a jihar Jigawa da ma kasar Hausa baki daya, haka kuma Sarkin na Hadeja shi ne a matsayin jagora ga dukkanin sauran masarautun da ke fadin jihar.

Yankin na Hadeja wadda ya kunshi manyan garuruwa masu tarihi a kasar Hausa, na da kananan hukumomi guda takwas da suka hada da Hadeja, Kafin Hausa, Auyo, Malam-madori, Kaugama, Kiri-kasamma, Birniwa da karamar hukumar Guri.

LABARAI MASU NASABA

Ganduje Ya Ambaci Sunan Sarki Sanusi Da Matsayin Sarkin Kano

Yadda Muka Magance Rikicin Kabilanci Da Shaye-shayen Matasa A Masarautarmu —Sarkin Shukura

Yankin Hadeja wadda ke Gabashin jihar ta Jigawa, Allah ya albarkace shi da masu ilimin addini da na zamani, ga kasar noma da kasuwanci, manyan ma’aikata a matakin kasa da jiha baki daya, wadda hakan ya sanya yankin bunkasa fiye da kowanne yanki a jihar.

Dangane da kafuwar masarautar kuwa, tarihi ya nuna cewa, yankin na Hadeja na da dimbin tarihi tun Kafin zuwan turawan mulkin mallaka domin kuwa ko a wancan lokaci, Hadeja Masarauta ce mai kunshe da Jarumai, Attajirai da Masana illimi.

Tarihi ya bayyana cewa tun kimanin shekarar 11,000, Habe ke mulki a yankin Garun-Gabas wadda ke karkashin karamar hukumar Malam[1]madori a yanzu, kuma sun yi fitattu kuma jaruman Sarakuna masu yawa wadanda suka hada da Sarki Kankarau, Asawa, Mamman Bako, Kawu, Baude, Musa da Kuma Abubakar.

Haka kuma tarihi ya bayyana cewa, a shekarar 1808 ne Fulani suka fara karbe mulki daga Habe a masarautar ta Hadeja kuma suka ci gaba da yi har zuwa wannan lokaci.

“A Lokacin Sarkin Hadejia na Habe Abubakar ne Fulani suka zo kasar Hadejia, a karkashin jagorancin Ardo Abdure dan Jamdoji, kuma Sarkin Habe Abubakar shi ne ya basu wurin zama, kana a zamanin Sarkin Fulani Sambo suka dawo Inda fadar Hadejia take yanzu, kafin daga bisa su kwaci mulki a hannun Sarakunan Habe a karkashin tutar Jihadin Shehu Usmanu Danfodiyo”.

Sarakunan Fulani a masarautar ta Hadeja sun hada da Sarki Umaru Dan Ardo Abdure 1805 – 1808, Sarki Mamman Kankiya Dan Umaru 1808 – 1808, Sarki Sambo Dan Ardo Abdure 1808 -1845, sai kuma Sarki Garko Gambo Dan Sambo 1845 – 1847, Sarki Abdulkadir Dan Sambo 1847 – 1848, Sarki Sambo Dan Ardo Abdure 1848 – 1848 (Hawa na biyu).

Sai Kuma Sarki Buhari Dan Sambo 1848 – 1850 (hawan farko), Sarki Ahmadu Dan Sambo 1850 – 1851, Sarki Buhari Dan Sambo 1851 – 1863 (Hawa na biyu), Sarki Umaru Dan Buhari 1863 – 1865, Sarki Haruna Bubba Dan Sambo 1865 – 1885, Sarki Muhammadu Maishahada Dan Haru Bubba 1885 – 1906.

Sauran Sarakunan sun hada da Sarki Haru Mai Karamba Dan Muhammadu 1906 – 1909, Sarki Abdulkadir Dan Haru Mai Karamba 1909 – 1925, Sarki Usman Dan Haru Mai Karamba 1925 – 1950, Sarki Haruna Dan Abdulkadir 1950 – 1985, Sarki Abubakar Maje Dan Haruna 1985 – 2002, sai kuma Mai Martaba Sarki Dakta Adamu Dan Abubakar Maje wanda shi ne a kan karagar mulkin Masarautar Hadeja har zuwa yanzu.

Mai martaba Sarki Dakta Adamu Abubakar Maje ya kasance Sarki na 16 a jerin Sarakunan Fulani a Hadeja, kuma ya zama Sarki a ranar 14 ga watan Satumbar shekarar 2002, bayan rasuwar mahaifinsa a ranar 11 ga watan na Satumba.

Kafin rasuwar mahaifinsa ya nada shi a matsayin IYAN HADEJA na farko, a ranar 3 ga watan Janairun shekarar 1999 yadda daga bisani ranar Laraba 11 ga watan Satumba na shekarar 2002 kuma Allah ya yi wa mahaifin nasa rasuwa.

Sannan a ranar 14 ga watan Satumbar kamar yadda al’adar Masarautar ta amince a nada sabon Sarki Kafin kwanaki uku da rasuwar wadda ke karagar.

Don haka majalisar Sarki suka nada shi a matsayin sabon Sarkin Hadeja na 16 bayan amincewar gwamnatin wannan lokaci.

Haka kuma an yi bikin bashi Sanda a ranar 29 ga watan Maris 2003, wadda gwamnan jihar Jigawa a wannan lokaci Alhaji Ibrahim Saminu Turaki ya jagoranta kuma aka gudanar a filin wasanni na Hadeja.

Mai Martaba Sarki bayan an bashi Sandar jagorancin kasar Hadejia a karkashin tutar Shehu Usman Dan Fodiyo, yadda daga nan kuma shagulgulan biki suka fara.

Mai Martaba Sarki ya gudanar da kayatattun Hawa guda uku tare da gudanar da addu’o’i da karatun Alkur’ani a Masarautar.

Shi dai Mai Martaba Sarkin Hadeja an haife shi ne ranar 15 ga watan Oktoba na shekar 1960, a cikin birnin Hadejia a tsohuwar Jihar Kano.

Mai Martaba Sarki ya fara karatun firamare a shekar 1967 zuwa 1972 a Makarantar Abdulkadir Primary school Hadeja.

Daga bisani ya shiga Makarantar Sakandire ta Garin Ikot Ekpene Cross-riber a shekarar 1973 zuwa1976, sannan ya koma makarantar Sakandire ta Danbatta a shekarar 1976-1979.

Mai Martaba Sarki ya samu nasarar shiga Makarantar Gaba da Secondary ta school of Rural and social science da ke Rano a Jihar Kano a shekarar 1981- 1982, da kuma 1983-1985.

Mai Martaba Sarki ya fara aikin Gwamnati a tsohuwar Jihar Kano a ma’aikatar walwalar al’umma, a shekarar 1982-1988, sannan ya koma hukumar jindadi da walwalar Alhazai ta jihar Kano a shekarar 1988-1991.

Bayan da aka kirkiro Jihar Jigawa Mai Martaba Sarkin Hadejia ya koma hukumar jindadi da walwalar Alhazai ta jihar Jigawa a shekarar 1991-1998.

Sannan ya koma Ma’aikatar Kananan Hukumomi ta jiha a shekarar 1998- 1999. A wannan shekarar ne Mai Martaba Sarkin Hadejia Dakta Abubakar Maje Haruna ya nadashi sarautar IYAN HADEJA kuma dan majalissar Sarki kafin daga bisani kuma a nada shi a matsayin Sarkin Hadeja na 16.

Daga karshe jaridar LEADERSHIP Hausa da ma’aikatanta na taya Mai Martaba Sarki murna tare da fatan Allah ya kara wa Sarki lafiya da nisan kwana masu albarka.

Shekara 20
Mika'il Tsoho
+ postsBio
  • Mika'il Tsoho
    https://hausa.leadership.ng/author/mikail-tsoho/
    Cikar Gwamnoni Kwana 100 A Karagar Mulki: Me Aka Tabuka A Jigawa, Bauchi, Nasarawa, Gombe, Borno Da Yobe?
  • Mika'il Tsoho
    https://hausa.leadership.ng/author/mikail-tsoho/
    Mai Martaba Sarkin Hadeja Zai Cika Shekara 20 Kan Karaga

MASU ALAKA

Ganduje Ya Ambaci Sunan Sarki Sanusi Da Matsayin Sarkin Kano
Da ɗumi-ɗuminsa

Ganduje Ya Ambaci Sunan Sarki Sanusi Da Matsayin Sarkin Kano

May 5, 2026
Yadda Muka Magance Rikicin Kabilanci Da Shaye-shayen Matasa A Masarautarmu —Sarkin Shukura
Masarautu

Yadda Muka Magance Rikicin Kabilanci Da Shaye-shayen Matasa A Masarautarmu —Sarkin Shukura

January 3, 2026
Tarihin Daular Borno Da Sarakunanta (3)
Masarautu

Tarihin Daular Borno Da Sarakunanta (3)

January 12, 2025
Next Post
Jerin ‘Yan Wasa Mafi Tsada A Firimiyar Ingila

Jerin ‘Yan Wasa Mafi Tsada A Firimiyar Ingila

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Tarayya Ta Mayar Da Ofishin NAGGW Zuwa Kano Domin Yaƙi Da Hamada

Gwamnatin Tarayya Ta Mayar Da Ofishin NAGGW Zuwa Kano Domin Yaƙi Da Hamada

June 4, 2026
Mambobin NYSC 4, Soja da Mutum 1 Sun Rasu A Hatsarin Mota A Adamawa

Mambobin NYSC 4, Soja da Mutum 1 Sun Rasu A Hatsarin Mota A Adamawa

June 4, 2026
Sarki Sanusi II Ya Tuɓe Rawanin Mai Unguwar Rikadawa Kan Badaƙalar Fili

Sarki Sanusi II Ya Tuɓe Rawanin Mai Unguwar Rikadawa Kan Badaƙalar Fili

June 4, 2026
Tawagar Masanan Dakile Yaduwar Cututtuka Ta Sin Ta Isa DR Congo

Tawagar Masanan Dakile Yaduwar Cututtuka Ta Sin Ta Isa DR Congo

June 3, 2026
Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Bangaren Sauya Fannin Wuta, Noma, Da Muhalli

Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Bangaren Sauya Fannin Wuta, Noma, Da Muhalli

June 3, 2026
Han Zheng Zai Halarci Taron SPIEF Karo Na 29 A Rasha Tare Da Gudanar Da Ziyarar Aiki A Belarus

Han Zheng Zai Halarci Taron SPIEF Karo Na 29 A Rasha Tare Da Gudanar Da Ziyarar Aiki A Belarus

June 3, 2026
Majalisa Ta Nemi Tinubu Ya Canza Dabarun Yaƙi Da Ta’addanci Don Kawo Ƙarshen Kashe-kashe

’Yan Majalisar Tarayya 3 Sun Fice Daga APC Zuwa ADC da PRP

June 3, 2026
An Fara Watsa Shirye-Shirye Masu Taken “Sha’awar Xi Jinping Ga Al’adu” Da Sauran Fina-Finan Bayyana Labaran Sin A Kasar Laos

An Fara Watsa Shirye-Shirye Masu Taken “Sha’awar Xi Jinping Ga Al’adu” Da Sauran Fina-Finan Bayyana Labaran Sin A Kasar Laos

June 3, 2026
Tambuwal Ya Jajanta Wa Waɗanda Harin ’Yan Bindiga Ya Shafa A Sokoto, Ya Nemi A Ƙara Tsaro

Tambuwal Ya Jajanta Wa Waɗanda Harin ’Yan Bindiga Ya Shafa A Sokoto, Ya Nemi A Ƙara Tsaro

June 3, 2026
Gwamnatin Beijing Ta Amince Da Kafa Cibiyar Kirkire-Kirkiren Fasahar Lissafi Mai Nasaba Da Sararin Samaniya

Gwamnatin Beijing Ta Amince Da Kafa Cibiyar Kirkire-Kirkiren Fasahar Lissafi Mai Nasaba Da Sararin Samaniya

June 3, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.