A yau Alhamis ne aka fara gudanar da taron kaddamar da tsarin kawance na kafafen yada labarun kasashe masu tasowa da kuma dandalin yada labarai na bidiyo na duniya karo na 13 a Xi’an, da ke lardin Shaanxi a yankin arewa maso yammacin kasar Sin.
Shugaban Pakistan Asif Ali Zardari, da shugaban Sri Lanka Anura Kumara Dissanayake, da shugaban Uruguay Yamandú Orsi sun aika da wasikun taya murna tare da fatan taron zai samu cikakkiyar nasara.
An kaddamar da tsarin kawancen na kafafen yada labarun kasashe masu tasowa ne a wurin taron. Wannan tsarin yana da nufin habaka hadin gwiwa tsakanin kafofin watsa labarai a kasashe masu tasowa da kuma inganta karfin tasirin tattaunawa na “kasashe masu tasowa” ta hanyar bin ka’idojin haduwa don “ginawa da rabawa, da amincewa da juna da tallafawa, da neman daidaito yayin da ake kiyaye bambance-bambance, da hadin gwiwar mabambanta”. A halin yanzu, gidajen watsa labarai 528 daga kasashe da yankuna 114 sun shiga cikin tsarin kawancen. (Abdulrazaq Yahuza Jere)













