Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya (NAF) ta kashe daruruwan mayakan ISWAP a Mallam Fatori da Shuwaram na jihar Borno, tare da lalata sansanonin ƴan bindiga a Garin Dandi da Chigogo a Kwara, da kuma Zango Hill a Katsina. Mai magana da yawun NAF, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya bayyana cewa hare-haren an kai su ne a ranar 9 ga Nuwamba, 2025, bayan samun sahihan bayanan sirri daga jami’an leƙen asiri.
Ejodame ya ce a jihar Borno, rundunar ta kai hari kai tsaye ga mayaƙan ISWAP da ke cikin Tumbuns, bayan gano motocin su, da babura, da jiragen ruwa a gaɓar tafkin Chadi.
Ya ce an lalata sansanonin ƴan ta’addan, da wuraren ajiyar makamai da kayan aiki, tare da kashe da dama daga cikin yan ta’addan. Haka zalika, a jihohin Kwara da Katsina, jiragen sama sun kai hare-hare bisa bayanan sirri a sansanonin Garin Dandi, Chigogo, da Zango Hill, inda aka hallaka shugabanni da mayaƙa da dama.
- Sojoji Sun Fatattaki Boko Haram, Sun Ceto Mutane 86 Da Aka Sace A Borno
- Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi Bagudo Ya Shaƙi Iskar ‘Yanci Daga ‘Yan Bindiga
A wani sumame daban, rundunar ta gudanar da aikin leƙen asiri mai ɗauke da makamai (Armed Reconnaissance) a ƙarƙashin Operation Fansar Yamma a yankunan Zamfara, da Kebbi, da Kaduna, inda ta gano wasu yan ta’adda a kan babura a kusa da tsaunin Wam, suka yi ƙoƙarin tserewa, amma jiragen sama suka yi gaggawar sheƙe su.
Ejodame ya ce waɗannan hare-haren sun tabbatar da ƙarin kuzarin rundunar Sojin sama wajen murƙushe yan ta’addan bisa umarnin Air Marshal Sunday Kelvin Aneke, tare da tabbatar da cewa za a ci gaba da kai hare-hare domin hana su sake samun damar dawo wa a yankunan Arewa.














