Mazauna ƙauyen Na-Alma da ke Jihar Katsina sun koka kan faruwar hare-haren ‘yan bindiga da suka yi sanadin mutuwar mutane da kuma sace wasu.
Wani mazaunin ƙauyen, Alhaji Umar Usman, ya ce an kashe mutane biyu tare da sace wasu biyu a ranar Lahadi, kwanaki kaɗan bayan makamancin wannan hari da ya faru a makon da ya gabata.
- An Daddale Kulla Cinikin Sama Da Dala Biliyan 83 A Bikin CIIE Na Kasar Sin
- Sin Ta Harba Sabon Rukunin Taurarin Dan Adam Masu Zagaye Kusa Da Doron Kasa
Ya ƙara da cewa, aƙalla mutane biyar ne aka kashe tun daga Litinin da ta gabata.
Usman ya ce duk da rahotannin da aka kai wa jami’an tsaro, ba a ɗauki wani mataki ba, kuma yanzu mazauna ƙauyen suna rayuwa cikin tsoro saboda ‘yan bindigar na yawo ba tare da wani kalubale ba a daren kowace rana.
Ya kuma bayyana yarjejeniyar sulhu da ‘yan bindigar a matsayin shirme, yana mai cewa ta ba su dama ne kawai su sake haɗa kai.
Usman ya roƙi Gwamnatin Jihar Katsina da hukumomin tsaro su kawo musu ɗauki, domin hare-haren sun lalata noma da tilasta mutane da dama barin gidajensu.














