Ƙungiyar Boko Haram ta samu nasara a kan ISWAP a wani ƙazamin faɗa da duka tafka a yankin Tafkin Chadi.
Rahotanni sun bayyana cewa mayaƙan ɓangaren Bakoura Doro na Boko Haram sun kai wa ISWAP hari, inda suka kashe ɗaruruwan mayaƙa tare da ƙwace jiragen ruwa da dama da suka cika da makamai da kayan abinci.
- Ƴan Bindiga Sun Sace Mata 4 Masu Shayarwa, Da Shanu 50 A Kano
- Sin Ta Harba Sabon Rukunin Taurarin Dan Adam Masu Zagaye Kusa Da Doron Kasa
Rahotanni sun ce jiragen ruwa uku ne kawai suka kuɓuta ba tare da an ƙwace su ba.
A cewar majiyoyi, sama da mayaƙan ISWAP 170 ne suka mutu a faɗan, yayin da Boko Haram ta rasa mayaka huɗu.
Ƙungiyar ta kuma kama jiragen ruwa guda bakwai da makamai masu yawa.
Wannan faɗa na daga cikin mafi muni a watannin baya-bayan nan, yayin da ƙungiyoyin biyu ke fafatawa kan ikon hanyoyin kamun kifi, da hanyoyin fasa ƙwauri a yankin Tafkin Chadi.
Masana harkokin tsaro sun bayyana damuwa cewa ISWAP na iya kai farmakin ramuwar gayya a makonni masu zuwa.














