Hukumar Kula da Shige da Fice ta Ƙasa (NIS) ta sake samun nasarar lashe kambun zama gwarzuwar hukuma mafi ƙwazo a cikin hukumomin gwamnati a bangaren shawo kan korafe-korafe a watan Agustan 2022.
Majalisar da shugaban ƙasa ya kafa a a kan kyatata yanayin hada-hadar kasuwanci (PEBEC) ta sanar da hakan a wani rahoton da ta fitar na suna kokarin hukumomi, Ma’aikatu, rassan gwamnatin na watan Agustan 2022.
Kamar yadda jami’in hulɗa da jama’a na NIS, DCI Amos Okpu, ya bayyana a wata sanarwa da ya fitar yau Lahadi, domin inganta aiki da lamuran da suka shafi samar da kyakkyawan yanayi na hada-hada, PEBEC ta fitar da wani tsari domin gano kokarin ma’aikatu da hukumomin gwamnati ko gazawarsu tare da hanyoyin da suke bi wajen shawo kan matsalolin jama’a masu hulɗa da Ma’aikatunsu.
Ya ce, daga cikin hanyoyin aiki da majalisar PEBEC ta sanar akwai shafin intanet na reportgov.ng wanda jama’a za su rika samun damar tuntubar ma’aikatu da hukumomi domin shigar da korafe-korafe ko kokensu ko wata gazawar da suka gani da ta shafi wata hukuma kuma ana tsammanin ma’aikatar da lamarin ya shafa za ta amsa wannan korafin ko koken cikin awanni 72.
“Kan haka ne hukumar PEBEC ta gabatar da tsarin duba kokarin Ma’aikatu a wata-wata domin duba yadda aka yi kokari ko akasinsa don kyautata aiki bisa yadda aka tsara.
“Kan amsa korafin jama’a cikin hanzari kuma a kan lokaci ne ta ofishin kula da aiki ya sanya hukumar Immigration ta lashe kambun hukuma mafi kwazo a watan Agustan 2022.”
Da ya ke tofa albarkacin bakinsa kan wannan nasarar, Shugaban Hukumar Kula da Shige da Fice ta Ƙasa (NIS), Isah Jere Idris, ya nuna matuƙar jin daɗi da wannan nasara tare da yaba wa ƙoƙarin jami’ansa da suka zage damtse suka yi aiki sosai domin farfaɗo da tsarin aiki a kowane lokaci.
Ya ba da tabbacin cewa zai ci gaba da himma wajen tabbatar da walwalar jami’ai da kyautata yanayin aiki da saka wa jami’an da suka yi ƙoƙari daidai gwargwadon abin da hukumar take da shi a hannu.
Jere ya jawo hankalin al’ummar kasar nan da a kowani lokaci su riƙa sanar da hukumar duk wani abun da suka fuskanta na kalubale ko rashin bin ka’idar aiki daga wani jami’in hukumar domin daukar matakan da suka dace.
Idan za ku iya tunawa dai wannan lambar yabon da hukumar kula da shige da fice ta samu shi ne karo na hudu a wannan shekarar daga wajen PEBEC domin ta samu irinsa a watan Afrilu, Mayu da Yuni sai kuma Agusta.
Ita dai majalisar da shugaban ƙasa ya kafa a kan kyautata yanayin hada-hada (PEBEC) an kaddamar da ita ce domin inganta harkokin kasuwanci a Nijeriya, zuwa yanzu mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo yake jagorantar ta.
Wannan lambar yabo da NIS ta lashe ya ƙara fayyace namijin ƙoƙarin da hukumar bisa jagorancin shugabanta, Isah Jere Idris ke yi na kyautata mu’amala da abokan hulɗarta da kuma ƙwazon aiki.