Barkanmu da sake saduwa daku a wannan fili namu, a wannan makon zamu so jin ra’ayoyinku a kan sabon yajin aikin da Kungiyar Malaman Jami’o’i, ASUU ta kara shiga bayan shafe wata 6 ana ja-in-ja tsakaninta ga Gwamnatin Tarayya. Menene ra’ayinku a kan albashin wata shida da ASUU ta bukaci a biya mambobinta? Wane mataki yakamata Gwamnatin ta dauka?
Adamu Yunusa Ibrahim
Maganar gaskiya wannan yajin aiki da Kungiyar Malamai ta ASUU ke yi kaifin Gwamnatin Tarayya ne. Kasancewar babu ‘ya’yansu a Jami’o’in gida Nijeriya ne ya sa Sam harkar ilimin ba ta gabansu. Kamar yadda suka kashe makarantun Primary da Secondary, har ta kawo sai wadanda ba su da yadda za su yi ne su ke tura yaransu makarantun. Saboda babu kwararrun malamai babu kayan aiki babu azuzuwan da yara ke zama don daukar darasi, idan ma akwai ajin babu kujeru. Hakan ya sa duk mai son yarona ya yi karatu sai dai ya kai shi makarantar kudi. Haka su ke so su ma Jami’o’in Nijeriya su koma. Domin yajin aikin da ASUU ke yi, ba a kan inganta albashin malamai kawai ake yi ba. Akwai alkawuran da Gwamnati ta dauka wajen samar da kudin yin gine-ginen azuzuwa da daliban kwanan dalibai da dakunan Gwaje-gwaje da dakunan Karatu na zamani mai dauke da na’urorin zamani da yara za su yi bincike domin inganta karatunsu. Duk wadannan na daga cikin abubuwan da Gwamnati ta kasa yi a Jami’o’in gida Nijeriya. Wata matsalar kuma ita ce yadda su ke son yin mummunan karin kudin makaranta da zai gagari Dan me karas da Dan me Yalo, biyan kudin makarantar. Hakan ya sa ba tare da la’akarin komai ba, su ke ta bayar da lasisin bude sabbin Jami’o’i masu zaman Kansu. Da yadda dan Talakan kasa zai gagara yin karatun sai yaransu. Tunda su ne ke tsabar kudi a ajiye da kadarorin da wasu ma ba su san iyakar su ba. Batun biyan Albashin Malamai na wata shida da wasu wata shidan da za su zo nan gaba, wannan ko tantama babu wajibi ne a biya. Domin shi aikin koyarwa a Jami’a ba kamar aikin gidan Burodi ba ne. Aiki ne da ya tattaro mutane masu ilimi da fikira da kuma hangen nesa. Kamar yadda shugaban ASUU na kasa Farfesa Emanuel Osodoke ya bayyana cewa, “Ko gobe Gwamnati Na iya kawo Karshen yajin aikin idan tana so”. Allah ya taimaki kasarmu Nijeriya da Jami’o’in gida Nijeriya. Amin.
Kwamrade Adamu Yunusa Ibrahim, Malami a Cibiyar Nazarin Hausa, Jami’ar Usmanu Danfodiyo Sakkwato, Nijeriya.
Mahdee Bashir
To nikam tunda a Nijeriya muke kuma mun san matsalolin kasarmu, wanda hatta tsaro ko harkar lafiya bai dameta ba balle ilimi, Dubi ga wagga batu innine ASUU dancen kafewa bai taso ba, tunda sunsan ba lalle a biya musu bukatunsu ba, saboda haka ko don daliba sai su yi hakuri a lallaba har Allah yakawo mana mafita, wannan raayi nane
Yusuf Muhammad Jalingo
Ra’ayina a nan, shi ne lallai laifin gwamnati ne saboda kowa a karkashinta yake, kuma dimokradiyya ce ta kawo gwamnatin kuma kowa na da ‘yancin ya nemi hakkinsa ta hanyar da ta dace kamar yadda ASUU ta yi sai dai gwamnati ta ba mu kunya don ba ta yi abin da ya dace ba . ASUU ta nemi abubuwa har bakwai amma gwamnati bata tabuka komai ba saboda tana nuna ko inkula a kan wannan lamari.
Sani Ladan
To a gaskiya tun da farko ita gwamnati ta yi sakaci har abin ya kazance haka kuma wannan shike nuni da cewa mafi yawan ‘yansiyasarmu basa mutunta harkar ilimin cikin gida sun fi kaunar su tura ‘ya’yansu makarantun Turai, ‘amma duk da haka suma ASUU ya kamata su duba ‘ya’yan talakawa su sassauta bukatunsu don samun mafita domin wadannan shugabannin basu da imani ko na kwabo daya kuma ba damuwarsu ba ne idan makarantu za su kai sheka 3 ba a bude ba ,amma komai suke yi Allah yana ganinsu kuma yana jiransu za su tarad dashi.
Baban Khairat
Kamata ya yi Malam nan su yi hakuri su duba yanayi da dalibai suke ciki na zaman gida ga lokaci na tafiya su janye saboda kishin kasa tunda su gwamnati an rasa samu daidaito ta wajensu. Allah ya kyauta
Kamal Y. Iyantama
Da ASUU din da Gwamnati duk wasa da hankalin talakawa suke yi, dukkansu muradun kansu suke karewa. Talaka ka ci gaba da kai wa Allah kuka.
Abdurrashid Ahmad Abubakar
Wannan lamari ya zama Inna lillahi wa Inna ilaihirraji’un, Allah ya kawo mana mafita kawai amma dukansu ba sa yi domin talaka.
Umar Ibrahim Umar
Ya zama wajibi gwamnati ta biya malamai hakkinsu saboda da ace ‘yan majalisa ne suke ya yin yajin aiki kana ganin gwamnati za ta hana su albashi ne, dan wannan wani sabon rikici ne da gwamnati ta dauko wanda zai kawo tsaiko mai tsawo da zai hana ‘ya’yan talakawan da suka zabi gwamnati karatu a kasarsu
Nazifi Haruna Iliyasu
Ni dai a nawa ra’ayin kamata ya yi gwamnati ta biya albashin su na wata 6 kana a zauna kuma ayi sulhu domin kyautata wa ‘ya’yan talakawa suma su sami ilimi, tunda ita gwamnati tana ikirari cewa ita ai ta talakawa ne.
Salihu Adamu
ASUU masu taurin kai. Da tun 2009 sun tsaya da an wuce wajen.
Ibraheem Yunuz
Mu dai don Allah a taimaka a janye ko mun koma makaranta don cigaba da karatu,wallahi mun gaji.
It’z Sam Dambatta
Babu abinda za mu ce da Allah sai godiya amma indai har gwamnati domin talakawa take yi to yakamata ace an magance matsalar nan tuntuni da ba wannan batun akeyi ba.
Shamsi Umar Bakanike Dambatta
Toh mudai sai dai muce Allah ya kawo karshen wannan yajin aiki da wannan kungiya ta ASUU suke yi.