An tabbatar da mutuwar mutane 9 yayin da wasu 10 suka jikkata a wani mummunan hatsarin mota da ya afku a yankin Yangoji zuwa Abaji da ke babban titin Abuja zuwa Lokoja a birnin tarayya Abuja.
Jami’in kula da ilimin jama’a (CPEO) da hukumar kiyaye hadurra ta tarayya (FRSC), Bisi Kazeem, ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Lahadi.
- Barin Bata-gari Cikin Al’umma Na Iya Zama Matsala A Gaba (1)
- Yadda Ake Rubutu Da Word (WPS Office) A Wayar Hanu (I)
Kazeem ya ce hatsarin ya rutsa da wata motar Bas, Toyota Hiance, mai lamba KTG-450 KQ da kuma motar Howo Sino da misalin karfe 06:05 na safiyar Lahadi.
Ya ce bas din fasinja ta taho ne daga jihar Osun ta nufi jihar Katsina, amma abin takaici ta fada cikin motar da ke tsaye.
Ya kara da cewa, hatsarin ya afku ne a kauyen Sabon Gari da ke kusa da Gada Biyu, a kan titin Abaji zuwa Yangoji.
A cewarsa, hatsarin ya shafi motoci biyu ne kawai kuma dukkansu na kasuwanci ne.
“Mutane 22 ne hatsarin ya rutsa da su, dukkansu maza ne, goma sun samu raunuka, tara kuma sun mutu, an bayar da agajin farko ga biyu.
“Hukumar FRSC ta kwato N3,170, buhuna shida da wayoyin hannu daban-daban guda 4,” inji shi.