Dalibai 240 ne daga cikin 2,747 na Jami’ar fasaha ta Gwamnatin tarayya, Akure (FUTA), Jihar Ondo, za su kammala karatun Jami’ar ta digiri mai daraja ta daya yayin da makarantar za tayi bikin yaye dalibanta a karo na 36.
Mataimakin Shugaban Jami’ar, Farfesa Adenike Oladiji, shi ne wanda ya bayyana hakan a lokacin da aka yi taron manema labarai kafin lokacin bikin yaye daliban, ya ce dalibai 1,479 suka samu digiri mai fdaraja ta biyu ( mafi daraja),sai kuma dalibai 912, suma digiri mai daraja ta biyu ne sai dai kuma (yana bin bayan mafi darajar) yayin da dalibai 116, sun samu digiri mai daraja ta 3.
- Tinubu Ya Zuba Naira Tiriliyan 1.5 Don Bunkasa Noma Da Kayan Aiki Na Zamani
- Babban Taron Kawancen Sin Da Afirka Ya Nuna Hadin Gwiwa Kan Gudanar Da Tsarin Shugabancin Duniya Na Bai-Daya
Farfesa Oladiji ya bayyana cewar Akindunbi Aduragbemi Isaac daga sashen Cibil Engineering shi ne wanda ya fi kowa hazaka a Jami’ar domin yana da (CPGA) 4.98 daga cikin 5.0.
Kamar dai yadda mataimakin Shugaban jami’ar ya kara jaddadawa, har ila yau Jami’ar za ta bada Difiloma ta bayan kammala digiri ga dalibai 86, sai kuma masu digiri na biyu kan fasaha (Master of Tech) 627 yayin da 154 masu sun samu digiri na uku ne da aka fi sani da digirin digirgir.
Farfesa. Oladi ya yi karin haske na cewa dalibai fiye da 3,000 daga Jami’ar suna amfana da bashin hukumar bada tallafin karatu ta kasa (NELFUND).
Da yake bayanin kan hukumar “Ya ce da akwai rashin bayani dangane da ita hukumar NELFUND, wasu dalibai basu san da akwai ta ba. Akwai kuma wani tunanin da mutane suke yi mi zai sa su tafi makaranta akan bashi?
“Mutane da yawa basu son amsar bashin.Don haka idan mutane basu da yawa, wannan ba kuma yana nufin kamar gwamnatin ta gaza bane, lamarin ya kasance ne domin mutane da yawa basu bukatar neman a basu bashin. Yayin da nake wannan maganar, mai kulawa da harkokin dalibai ya ce akwai dalibai fiye da 3,000 da suke amfana daga shi tsarin na bada bashin kudin makaranta kamar dais hi mataimakin Shugaban Jami’ar ya bayyana,” the BC said.
Da yake bayyana Jami’ar fasaha ta gwamnatin tarayya dake Akure , FUTA a matsayin wadda tafiya tare da ita ne a duniya dangane da harkar data shafi ilimi, Farfesa.Oladiji ya ce, makarantar tana tafiya tamkar yadda mutane suke tunanin ko kallonta a matsayin wani wuri ne da ake samun ilimin Boko mai nagarta kamar yadda ya dace,bugu da kari kuma wani wuri ne inda mutum yake daukar mataki na irin yadda yake bukatar cikin ikon Allah ya kasance na dukkan wasu lamurran da suke da alaka da abubuwan da suka shafi karatu gaba daya.
‘’Jami’ar fasaha ta gwamnatin tarayya Akure babbar makaranta ce da ta yi suna musamman ma ta bangaren bincike kan lamurran da suka shafi bangaren ilimin fasaha,saboda a samu damar cimmar irin matsalolin da al’umma da duniya suke fuskanta.Hakan abin yake idan aka, tuna da lamarin daya shafi sauyin yanayi da kuma ilimin kimiyyar samaniya,aikin gona, Injiniya, Komfuta da kuma kwarewar lamarrran kafafen sadarwa na zamani.
“A Jami’ar fasaha ta gwamnatin tarayya Akure FUTA, mambobi na sassan ita Jami’ar da daibai suna kara kasancewa masu daraja ne da amfani kan lamurran daban- daban a kan lamarin daya shafi karatu ko bada/ koyar da ilimi a duniya, inda suke kasancewa sai an yi tafiya tare da su musamman ma, ta bangaren yin bincike da sanin yadda za a bunkasa abinda aka gano hanyar da za ayi shi. Hakanan ma FUTA bata tsaya ta yi kasa a gwiwa ba domin kuwa tana bada gudunmawa wajen karin haske kan hanyoyin da za abi wajen samar da isasshen abinci a Nijeriya kamar dai yadda Oladiji ya yi nashi karin hasken,”.














