Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya buƙaci al’ummar Faruruwa a ƙaramar hukumar Shanono da su ƙarfafa tsaro tare da haɗa kai da jami’an gwamnati domin daƙile hare-haren ƴan bindiga da ke shigowa daga jihar Katsina. Sarkin ya kai ziyara ta musamman ne yayin da harin ƴan daba ya yi ƙamari a watannin baya, abin da ke sanya jama’a cikin fargaba.
Sarki Sanusi ya bayyana cewa hare-haren sun janyo kashe-kashen mutane, da sace-sace, da satar dabbobi, wanda ya sa ya fito da kansa domin jajanta wa mazauna yankin da kuma ƙarfafa musu gwuiwa. Ya ce gwamnatin jihar ta ƙara yawan jami’an tsaro, ta ba su motocin sintiri da kayan aiki domin kare yankunan da ke da rauni.
Sarkin ya kuma buƙaci al’ummar yankin da su ƙarfafa tsaro ta hanyar haɗawa da tsare-tsaren ƴan sa-kai da ake da su, domin su zama garkuwa tare da jami’an tsaro. A cewarsa, hakan zai taimaka wajen hana mahara samun damar kutsawa cikin Sauƙi. Ya kuma gargaɗi kauyukan Katsina da ke makwabtaka da kada su riƙa shiga yarjejeniyar sulhu da ƴan bindiga wadda ke basu damar kai wa Kano hari su koma.
Shugaban ƴan sa kai (Faruruwa Security Community Forum), Alhaji Yahya Bagobiri, ya yabawa ziyarar Sarkin, yana mai cewa zuwan nasa ya haifar da gaggawar gudunmawa ta tura ƙarin Sojoji zuwa manyan hanyoyin shigowa yankin. Ya ce hakan ya ƙara ƙwarin gwuiwar jama’a kuma ya rage tsananin tsoro da suke fama da shi.














