Rundunar Ƴansandan birnin tarayya ta bayyana cewa babu wani rahoto ko bayanin da ta samu game da yunkurin kashe laftanar Ahmed Yerima, jami’in Sojin ruwa da ya yi taƙaddama da Ministan Abuja, Nyesom Wike, kan wani fili da ake jayayya kansa a Abuja kwanakin baya. Jami’ar hulɗa da jama’a ta rundunar, SP Josephine Adeh, ta fitar da sanarwar ne a ranar Litinin tana mai ƙaryata labarin da ya yaɗu a kafafen sada zumunta.
Adeh ta ce babu wani lamari da ya faru ko aka rubuta a koda ɗaya daga cikin wata ƙaramar hukumar da ke cikin birnin, don haka ta buƙaci jama’a da su yi watsi da labarin saboda ba shi da tushe. Ta ƙara da cewa irin waɗannan labaran karya na iya tayar da hankalin jama’a da haddasa tashin hankali ba tare da dalili ba.
- Laftanal Yarima Ya Tsallake Rijiya Da Baya A Abuja
- Bayan Shekaru 20 Yana Bacci, Yariman Saudiyya Ya Rasu
Rundunar ta kuma shawarci jama’a da su yi taka-tsantsan wajen yaɗa bayanan da ba su tabbata ba, tare da samar da sahihan hanyoyin samun bayanai idan wani abu ya taso. Ta ce kare lafiyar jama’a da tabbatar da zaman lafiya shi ne babban aikin da rundunar ta sa a gaba.
A ƙarshe, rundunar ta buƙaci mazauna Abuja da su riƙa kai rahoton duk wani abin da suka ga ya saɓa wa tsaro ga ofishin ƴansanda mafi kusa, ko kuma su tuntuɓi shalƙwatar rundunar ta hanyar layukan gaggawa: 08032003913 da 08068587311 domin samun kulawa cikin gaggawa.














