Sashen jigilar kayayyaki na kasar Sin ya gudanar da hada-hadar kunshin sakonni biliyan 162.68 a cikin watanni 10 na farkon shekarar 2025, wanda ya nuna an samu karuwar kashi 16.1 cikin dari a mizanin shekara-shekara, kamar yadda alkaluman hukuma suka nuna a yau Talata.
A cewar hukumar kula da gidan waya ta kasar Sin, babbar masana’antar gidan waya ta kasar wacce ta kunshi sashen aikewa da sakonni, ta gudanar da jigilar kunshi sakonni biliyan 177.25 a tsakanin wannan lokaci, wanda ya nuna an samu karuwar kashi 14 cikin dari idan aka kwatanta da makamancin wannan lokacin a shekarar 2024. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
ADVERTISEMENT














