Ma’aikatar tsaron kasar Sin ta yi Allah wadai da aniyar kasar Amurka ta sayarwa yankin Taiwan makamai, bayan da Amurkan ta ayyana shirin cinikayyar makamai na dala miliyan 330 da bangaren na Taiwan. Ma’aikatar ta ce Sin za ta dauki dukkanin matakan da suka wajaba na kare ikon mulkin kai da martabar yankunanta.
Yayin da yake amsa tambayar da aka yi masa game da hakan, a taron manema labarai na jiya Litinin, kakakin ma’aikatar Zhang Xiaogang, ya ce cinikayyar makamai tsakanin Amurka da yankin Taiwan ta yi matukar keta hurumin manufar nan ta kasar Sin daya tak a duniya, da ma sanarwa uku da kasashen Sin da Amurka suka daddale, kana matakin matukar tsoma baki ne cikin harkokin cikin gidan Sin, ya kuma keta ikon mulkin kai da moriyar tsaron kasa. Kazalika, yana aikewa da mummunan sako marar dacewa ga ‘yan aware masu rajin neman ‘yancin kan yankin Taiwan.
Kakakin ya kuma kara da cewa, duk wani mataki na yunkurin taimakawa manufar neman ‘yancin kan Taiwan ta amfani da matakan soji, ba abun da zai kawo illa haifarwa kai mummunan sakamako, kuma yunkurin amfani da Taiwan a matsayin makamin dakile kasar Sin ba zai taba yin nasara ba. (Saminu Alhassan)














