Dakaru da dama sun ji rauni bayan da ‘yan ta’adda suka yi musu kwanton ɓauna yayin da suke aikin ceto daliban Makarantar Sakandare ta ‘Yan Mata ta Gwamnati, Maga, da aka sace a Jihar Kebbi.
Harin ya zo ne sa’o’i 24 kacal bayan da Babban Hafsan Sojan Kasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya umurci sojojin rundunar ‘Operation Fasan Yamma’ da su “yi duk mai yiwuwa” kan ceto yaran daga hannun ‘yan bindiga
Shaibu ya jaddada muhimmancin aikin ceton, yana mai cewa, “Dole ne mu ci gaba da bincike ba dare ba rana. Dole ne mu nemo waɗannan yaran.”
COAS ya kuma umurci kwamandojin da su dogara da amfani da bayanan sirri don samun nasarar aiki, yana mai gargadin cewa, “Da zarar kun sami bayanai kan wani abu makamancin haka, ku yi aiki da kwarewa wajen yanke shawara. Wannan ba wai kawai dangane da kiyaye mutuncinmu ba ne; wannan shi ne nauyin da ya rataya akanmu.”














