Hukumar babban birnin tarayya Abuja, FCTA a ranar Litinin, ta rusa wani gidan shakatawa (Spotlight Garden Events and Recreation) a gundumar Wuye da ke Abuja bisa zargin keta dokar lokacin rufe wuraren shakatawa da lambuna.
Mai kula da tsare-tsare na hukumar kula da harkokin babban birnin tarayya Abuja (AMMC), Mista Umar Shuaibu, wanda ya jagoranci tawagar rusau din, ya shaida wa manema labarai cewa babu gudu babu ja da baya kan aiwatar da dokar rufe wuraren shakatawa da lambuna daga karfe 7 na dare a Abuja.
Shu’aibu ya ce, za a gurfanar da wanda ke kula da lambun a gaban kotu bisa saba ka’ida, wacce ta yi sanadin mutuwar wani wanda baiji bai gani ba.
“A makon da ya gabata a wani wurin shakatawa da ake kira Spotlight Garden Events and Recreation a gundumar Wuye, mahukunta lambun sun karya ka’idar rufe lambun da aka gindaya kar a wuce karfe 7 na dare.
“Wannan ya ja hankalin ‘yan bindigar da ke dauke da makamai, inda suka bindige wani babban jami’in tsaro. Da ba su keta doka ba, da an kauce wa kisan,” inji shi.
Kwanan nan ne mahukunta babban birnin tarayya Abuja suka haramtawa wuraren shakatawa da Lambuna gudanarwa sama da karfe 7 na yamma kamar yadda aka tanada a cikin Dokokin shakatawa na 2005.