Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya ce a shirye kasar Sin da Afrika ta Kudu suke, su mara wa juna baya da zurfafa hadin gwiwar moriyar juna a tsakaninsu.
Li Qiang ya bayyana haka ne jiya Lahadi, a ganawarsa da mataimakin shugaban Afrika ta Kudu Paul Mashatile a gefen taron kungiyar G20 da ya gudana a ranakun Asabar da Lahadi.
A cewar Li Qiang, a shirye Sin take ta inganta hada hannu da Afrika ta Kudu da taimakawa karin kayayyaki masu inganci da karfin takara na kasar, shiga kasuwar kasar Sin ta hanyar tattaunawa da cimma yarjejeniya kan hadin gwiwar tattalin arziki domin samun ci gaba na bai daya da gaggauta ba Afrika ta Kudu damar cin gajiyar manufar kasar Sin ta soke haraji da kaso 100 bisa 100 kan kasashen Afrika dake da huldar diplomasiyya da ita.
Ya ce Sin tana taimakawa kamfanoninta masu karfin takara su zuba jari a Afrika ta Kudu da bunkasa hadin gwiwa a bangarorin da suka shafi makamashi mai tsafta da ababen hawa da kiwon lafiya da tattalin arziki na dijital da kayayyakin more rayuwa, da nufin fadadawa da daukaka hadin gwiwar kasashen biyu, domin kara bayar da gudunmuwa ga aikin zamanantar da kasashen biyu.
A nasa bangare, Paul Mashatile wanda ya nanata goyon bayan kasarsa ga manufar kasar Sin daya tak a duniya, ya ce a shirye Afrika ta Kudu take ta dauki aiwatar da manufar Sin ta soke haraji na kaso 100 bisa 100 ga kasashen Afrika a matsayin wata dama ta zurfafa dangantaka a bangarorin tattalin arziki da cinikayya da ayyukan masana’antu da na gona da tattalin arzikin digital da kare muhalli, domin inganta musaya tsakanin jama’arsu, ta yadda za a ci gaba da bunkasa raya dangantaka ta kowace fuska tsakanin kasashen biyu a sabon zamani. (FMM)














