Gwamna Nasir Idris na Jihar Kebbi ya yi kira ga sojoji da su canza salon da suke amfani da shi wajen magance rashin tsaro.
Gwamnan ya fadi haka ne lokacin da ya karbi bakuncin Kakakin Majalisar Wakilai, Hon Tajudeen Abbas, ranar Litinin a gidan Gwamnati da ke Birnin-Kebbi.
- Sin Ta Yi Alkawarin Zurfafa Dangantaka Da Afrika Ta Kudu
- ‘Yan Ƙunar Baƙin Wake Sun Kashe Jami’ai 3 A Hedikwatar Rundunar Tsaro Ta Pakistan
Gwamnan ya kuma sake nanata kiransa na a binciki janye sojojin da aka tura zuwa Makarantar Sakandare ta ‘Yan Mata ta Gwamnati, Maga, mintuna kafin ‘yan bindiga su sace ‘yan mata ‘yan makaranta 25.
“Ta yaya ‘yan bindiga sama da 500 za su iya fitowa akan babura a manyan hanyoyinmu ba tare da wata barazana daga jami’an tsaro ba? Muna sauke nauyin da ke kanmu na tallafawa hukumomin tsaro, muna ba su kayan aiki, mun saya musu motoci sama da 100 amma tsarin yadda suke tsaron kasa baya aiki.
“Da mun san za su bari ‘yan bindiga su kwashe ‘yan matanmu, da ba mu saurari shawarar da suka ba na tura jami’an tsaro ba. Da mun rufe makarantar kawai.
“Jiya an kwashe a Kebbi, yau a Neja da Kwara; wa ya san wace jiha za a je gobe? Dole ne mu tabbatar da cewa an magance wannan rashin tsaron.” In ji Gwamna Nasir














