Sashen Bayar da Kariya na Musamman na Rundunar ‘Yansandan Nijeriya ya umarci dukkan jami’an da ke bayar da kariya ga manyan mutane (VIP) a duk fadin kasar da su koma sansaninsu.
Wannan ya biyo bayan umarnin da Shugaba Bola Tinubu ya bayar a ranar 23 ga Nuwamba, wanda ya bayar da umarnin janye jami’an ‘yansandan da aka ɗaura wa alhakin tsaron VIP a fadin kasar nan take.
- Gwamnonin Kudu Maso Yamma Sun Sake Jaddada Buƙatar Kafa ’Yansandan Jihohi
- Sojoji Sun Kama Ɗan Bindiga A Taraba
A cikin wata sanarwa da Kwamandan Rundunar SPU Base 16 da ke Legas, Neji Veronica, ya sanya wa hannu, kuma mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga, ya ɗaura ta a shafinsa na X a ranar Talata, an umurci dukkan jami’an da abin ya shafa da su koma sansaninsu kafin ranar 24 ga Nuwamba ta kare.
A karkashin sabon tsarin, Tinubu ya ce, manyan mutane da ke bukatar kariyar tsaro, su nema daga jami’an Hukumar Tsaron Jama’a ta Nijeriya (NSCDC), maimakon dogaro da jami’an ‘yansanda.














