Kasar Sin ta harba kumbon Shenzhou-22 mai binciken sararin samaniya daga cibiyar harba tauraron dan adam ta Jiuquan dake arewa maso yammacin kasar a yau Talata, wanda hakan ya zama aikin harba kumbo na gaggawa karon farko a shirin kasar na harba kumbo mai dauke da ’yan sama jannati.
Kumbon ya fice daga rokar da aka harba shi a ciki, kana ya shiga da’irar sararin samaniyar da ake bukata. Hukumar kula da harba kumbuna masu dauke da ’yan sama jannati ta kasar Sin ta ayyana kammala aikin harba kumbon cikin nasara. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
ADVERTISEMENT














