Ma’aikatar kasuwancin kasar Sin ta ba da kididdiga jiya Talata cewa, yawan jarin da Sin ta zuba kai-tsaye a ketare ya wuce Yuan triliyan 1 a farkon watannin 10 na bana , wanda ke nuni da karuwar kashi 7% idan aka kwatanta da makamancin lokaci na bara.
A cikin wadannan adadi, yawan jarin da ba na hada-hadar kudi ba wanda masu zuba jari na Sin suka zuba wa kamfanoni 9,553 na ketare daga kasashe da yankuna na duniya 152, ya wuce Yuan biliyan 872.6, wanda ya karu da kashi 6%.
Bugu da kari, a cikin farkon watanni 10 na wannan shekara, yawan jarin da ba na hada-hadar kudi ba, da kamfanonin Sin suka zuba a kasashen dake bin shawarar “ziri daya da hanya daya” ya wuce Yuan biliyan 234.15, wanda ya karu da kashi 22.3%. (Amina)














