Mai Ba da Shawara Kan Tsaro Ga Gwamnatin Jihar Kogi, Kwamanda Jerry Omodara (mai ritaya), ya ƙaryata jita-jitar cewa ‘yan bindiga sun sace ɗaliban Makarantar Sakandare ta Kiri da safiyar Laraba.
Wata jaridar kafar intanet ce ta bayyana cewa, ‘yan bindiga sun kai hari Makarantar Sakandare ta Kiri da ke Aiyetoro Kiri, karamar Hukumar Kabba Bunu ta Jihar Kogi, a safiyar Laraba, a wani yunƙurin sace wasu dalibai.
- Ana Raɗe-raɗin Sojoji Sun Yi Juyin Mulki A Guinea-Bissau
- Kamfanin Kasar Sin Ya Ba Da Gudummawar Kwamfutoci Da Magungunan Zazzabin Cizon Sauro A Kudancin Benin
Ta ƙara da cewa, mambobin ƙungiyar ‘yan banga ta Kiri waɗanda suka yi gaggawar kai ɗauki, sun yi nasarar ceto dukkan ɗaliban da aka sace a yayin harin.
Jaridar ta rahoto cewa, majiyoyi daga cikin al’ummar yankin sun shaida cewa, babu wani ɗalibi da ya rage a hannun ‘yan bindigar.
Sai dai, wani ɗan banga da wani mazaunin yankin da ake kira Bahaushe, sun rasa ransu sakamakon mummunan harin.
Amma a cikin martanin gaggawa, Kwamanda Omodara ya ce labarin ƙarya ne, yana mai jaddada cewa, gwamnati tana bin diddigin waɗanda ke wallafa labaran ƙarya a shafukan sada zumunta.
ADVERTISEMENT














