Yusuf Maitama Tuggar, wanda yake ministan da ke kula da harkokin wajen Nijeriya kuma ɗan Jihar Bauchi ya yi alhinin rasuwar babban malamin addinin Islama Sheikh Dahiru Usman Bauchi da Allah Ya yi wa rasuwa.
Tuggar ya bayyana wannan rashin a matsayin wanni babban giɓi musamman ma a fannin karantawar addinin Musulunci a Nijeriya.
“Lallai wannan rashin rashi ne da baza a taɓa mantawa da shi saboda yadda Sheikh Dahiru Bauchi ya bayar da gudunmawa wajen karantar da al’umma da iliminsa da dukiyarsa da lafiyarsa”
Tugga ya mika sakon ta’aziyyar rasuwarsa ga Iyalansa da ‘yan uwa da abokanan arziki da dalibansa kan wannan rashi da aka yi. Sannan ya yi addu’ar Allah ya jiƙansa ya gafartamasa ya sa aljanna ce makoma.














