Ofishin yada Labarai na majalisar gudanarwa ta kasar Sin, ya fitar da wata takardar bayani mai taken “Kayyade makamai, rage Soji da hana yaduwar makamai a sabon zamani na Sin”.
Takardar ta bayyana cewa, Sin ta gabatar da wannan takarda ce don bayyana manufofinta na kayyade makamai, da rage soji da hana yaduwar makamai a sabon zamani, da gabatar da shawarwarinta na tabbatar da tsaron sararin samaniya, da yanar gizo, da fasahar kirkirarriyar basira ta AI, da niyyarta ta kiyaye zaman lafiya da tsaro a duniya, da kuma kira ga kasashen duniya da su hada kai don cigaba da shirin kayyade makamai na kasa da kasa, da amfani da fasaha da kimiya yadda ya kamata.
Takardar mai sassa 5, ta kunshi batun yanayi mai sarkakiya da tsanani a bangaren tsaron kasa da kasa, da na kayyade amfani da makamai, da matsayin manufofin kayyade makamai na Sin a sabon zamani, da shiga tsakani mai ma’ana a shirin kayyade makamai na kasa da kasa, da jagorantar aikin lura da tsaron duniya a sababbin fagage, da karfafa hadin gwiwar kasa da kasa wajen hana yaduwar makamai da amfani da fasaha cikin lumana. (Amina Xu)














