Uwargidan Gwamnan Zamfara, Hurriya Dauda Lawal, ta jagoranci ƙaddamar da taron Kwanaki 16 na Yaƙi da Cin Zarafin Mata na 2025 a Funtua, tare da haɗin gwuiwar Ma’aikatar Mata da ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam. Ƙungiyoyin da suka shiga cikin shirye-shiryen sun haɗa da ƙungiyar ceto ta Duniya, da Premium Vanguard International da kuma ƙungiyar Kula da Lafiyar Haihuwa, waɗanda suka fara taron da gagarumin gangamin wayar da kai a unguwanni da makarantu.
A jawabinta, Hurriya Lawal ta bayyana cewa an tsara ayyukan wannan shekarar domin ƙara faɗakar da mata, matasa da iyaye kan illolin cin zarafi, musamman na yanar gizo wanda ke ƙaruwa a tsakanin al’umma. Ta ce shirin zai mayar da hankali kan ilmantar da ɗalibai, da amfani da kafofin watsa labarai da kuma jan hankalin masu ruwa da tsaki domin tabbatar da cewa ana kai rahoton duk wani nau’in cin zarafi cikin gaggawa.
- Jami’an APC 3 A Jihar Zamfara Da Aka Dakatar Sun Maka Jam’iyyar A Kotu
- Ƴan Bindiga Sun Sace Mutane 14 A Wani Sabon Hari A Zamfara
Uwargidan Gwamnan ta nanata cewa cin zarafi ta hanyar kafafen sada zumunta ya zama sabuwar barazana ga lafiyar mata da marasa ƙarfi, don haka akwai buƙatar haɗin kai tsakanin hukumomi da al’umma wajen kare waɗanda ke cikin haɗari. Ta yi kira ga iyaye, da malamai da shugabannin al’umma da su zama tubalan kariya ga mata da yara ta hanyar tashi tsaye wajen kai rahoto da kuma goyon bayan waɗanda abin ya shafa.
Taken taron na bana, shi ne “Cin zarafi a kafafen sada zumunta yana daidai da cin zarafi a zahiri,” ya karkata hankali kan buƙatar ɗaukar duk wani cin zarafi na yanar gizo da muhimmanci iri ɗaya da wanda ake aikatawa a zahiri.














