Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kafa wani kwamiti da zai sake duba bukatun kungiyar malaman jami’o’i ta kasa, ASUU.
Kungiyar ta shiga yajin aikin ne tun a watan Fabrairu domin neman Gwamnati ta sake farfado da jami’o’in gwamnati, ta biya malaman kudaden alawus-alawus na ilimi sannan kuma ta amince da tsarin biyan albashi ga Malaman Jami’o’i ta hanyar amfani da UTAS ba IPPIS ba, da dai sauran wasu bukatu.
Ana tsaka da yajin yajin aikin, gwamnati ta kawo tsarin ‘Ba aiki, ba biyan albashi’ domin tilasta wa malaman janye yajin aikinsu, inda ta dage cewa ba za a biya malaman jami’o’in albashi ba na tsawon lokacin da suka shafe suna yajin aikin.
Wannan kudirin gwamnatin, ya kara hargitsa Malaman, inda suka yi fatali da kudirin sannan kuma suka kara wani sabon wa’adi na cigaba da yajin aikin.