An rufe taron baje kolin cinikayyar hidima na kasa da kasa na kasar Sin CIFTIS na shekarar 2022 jiya Litinin, 5 ga wata.
Taron na tsawon kwanaki 6 ya samu halartar kamfanoni masu karfi guda 507 da kasashe 10 wadanda karo na farko suka shirya harkoki don yayata kansu.
Kwarya-kwaryar kididdiga ta nuna cewa, an cimma sakamako iri daban daban 1339 a yayin taron, ciki hada da wasu 173 da aka kaddamar da su karo na farko a duniya, adadin da ya karu da guda 34 bisa na taron na shekarar 2021, lamarin da ya kafa tarihin taron.
Yadda yawan fasahohi da kayayyaki masu nasaba da kirkire-kirkire suke ta karuwa a yayin taron na CIFTIS, ya nuna muhimmancin kirkire-kirkire cikin cinikayyar hidima.
Alkaluman taron harkokin cinikayya da bunkasuwa na MDD sun nuna cewa, a cikin cinikayyar hidima ta kasa da kasa, yawan hidimar fasaha da bayanai, hidimar hakkin mallakar fasaha da harkokin nazari wadanda suka shafi kirkire-kirkire ya karu zuwa 18% a shekarar 2020 daga 11.4% a shekarar 2005.
A bana ake cika shekaru 10 da fara gudanar da taron na CIFTIS. A cikin shekaru 10 da suka wuce, yawan wadanda suka yi hadin gwiwa da kasar Sin ta fuskar cinikayyar hidima ta kasa da kasa ya wuce kasashe da yankuna 200.
Yayin da aka kawo tsaiko ga dinkewar duniya, kana rikici na ta abkuwa a shiyya-shiyya, taron CIFTIS ya kara samun mahalarta.
Dalilan da suka sa haka su ne, da farko, kasuwar kasar Sin tana jawo hankali sosai, na biyu kuma, taron na CIFTIS ya zama muhimmiyar alamar yadda kasar Sin take kara bude kofa ga kasashen ketare, zurfafa hadin gwiwa, da ba da jagora kan yin kirkire-kirkire, na uku kuma, taron na CIFTIS ya nuna aniyar kasar Sin ta kara azama kan dinkewar tattalin arzikin duniya, lamarin da kasashen duniya ke matukar bukata yanzu haka. (Tasallah Yuan)