ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, December 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Morocco: Kasar Da Ke Neman Zama Fuskar Kwallon Ƙafa A Duniya

by Abba Ibrahim Wada and Sulaiman
3 weeks ago
Morocco

Kasar Morocco, inda za a gudanar da gasar cin kofin nahiyar Afirka, kasar da take can kurya a yankin arewa maso yamma a nahiyar Afirka – tana tsakanin tekun Atalantika da na Bahar Rum, inda take da al’umma miliyan 36.9.

Birnin Rabat, birni na bakwai mafi girma a kasar shi ne babban birnin kasar, yayin da birnin Casablanca ke zaman babbar cibiya tattalin arziki da harkokin kudi na kasar mai arzikin dabino.

Kasar tana da gabar teku mai tsawon kilomita 3,500, sannan ta ratsa tsaunukan Atlas, ga ta kuma a kusa da Hamadar Sahara. Moroko tana da wurare na shakatawa a bakin tekun Bahar Rum da kuma na Atalantika da tsaunuka na hamada da wurare masu dausayi da shukoki da kuma jigayi.

ADVERTISEMENT

Gasar Cin Kofin Afirka ta 2025, wadda kasar za ta karbi bakunci a karo na biyu, harka ce ta wasa da kasar ke dauka da muhimmancin gaske a ‘yan shekarun nan domin a yanzu kasar ta dukufa wajen kasha makudan kudade wajen bunkasa harkokin wasannin kwallon kafa.

Kamar dai ga sauran kasashen Afirka wasan kwallon kafa shi ne ya fi farin jini a Moroko. Wasan kwallon kafa wasa ne da ke zaman wata alama ta hada kan kasar da kuma tasirin kasar a nahiyar Afirka – inda bajintar da tawagar kasar, ta yi a gasar cin kofin Duniya ta 2022, ta kara jaddada ta.

LABARAI MASU NASABA

Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Addinin Musulunci shi ne addinin da ke matsayin na gwamnati a Moroko, inda sama da kashi 99 cikin dari na al’ummar kasar Musulmi ne, ‘yan Sunni da ke bin mazhabin Malikiyya. Amma duk da haka doka ta 6 ta kundin tsarin mulkin kasar ya tabbatar da ‘yanci da bayar da dama mutum ya yi wani addinin da yake so.

Daga cikin mabiya addinan da ba su da rinjaye akwai Kiristoci da suke kashi 1 cikin dari na yawan al’ummar kasar sannan akwai kuma al’ummar Yahudawa da suke da yawan digo biyu (0.2) cikin dari ko kuma a ce mutum dubu ashirin (20,000) a cikin al’ummar kasar.

Moroko na amfani da tsarin mulki na mulukiyya mai amfani da majalisar dokoki, karkashin shugabancin sarki, na masarautar Alawi, da ke shugabantar kasar tun tsakiyar karni na 17. Masu sarautar suna da asali na addini, kasancewar an yi imanin cewa suna da alaka da iyalan gidan Annabi Muhammad (S.A.W), da kuma shugabanci da suka ratso tun mulkin-mallaka har zuwa zamanin ‘yancin kai.

Wannan dorewa a mulki ta sa masarautar ta Moroko ta kasance ta biyu mafi dadewa da har yanzu take mulki, bayan ta Japan. Sarki Mohammed na shida yana da shekara 36, a lokacin sunansa Sidi Mohammed, kasancewarsa babban dan sarki ya gaji mahaifinsa Sarki Hassan na biyu, wanda ya rasu ranar 23 ga watan Yuli, 1999.

Sarki Mohammed na shida ya gudanar da sauye-sauye da dama a kasar tun lokacin da ya karbi jagorancin kasar.

A tarihin Moroko ta yi babban birni na kasa har guda hudu. Fez, da Marrakech, da Meknes, sai kuma na baya-bayan nan Rabat, kuma dukkannin wadannan birane sun kasance mazaunar gwamnati, daga zamanin masarauta zuwa masarauta da kuma yanayi. Kowanne daga cikin biranen hudu na dauke da abubuwa na tarihi da suka danganci siyasa da tattalin arzibi da makamantansu.

Jami’ar Kuaraouiyine (ko Al-Karawiyyin), wadda aka kafa tun a shekarar 859 a birnin Fez, ita ce mafi dadewa da har yanzu take aiki a duniya, kamar yadda hukumar ilimi da kimiyya da al’adu ta duniya, UNESCO, da kuma kundin bajinta na duniya (Guinness World Records), suna nuna.

Wannan jami’a ta horas da malaman addinin Musulunci da masana da dama tsawon karni daban-daban inda ta taimaka wajen bunkasar Moroko da kuma al’adun Musulunci. Dakunan karatun wannan jami’a na dauke da takardu da muhimman littattafai masu tarihi.

Man Argan wanda ake yi daga ‘ya’yan itacen argan, bishiyar da ake samu a yankin kudu maso yammacin Moroko, na da daraja sosai kuma ya kasance wata alama ta kasar. Man wanda ake nema sosai wanda ake abinci da shafa, a yanzu ya zama wata alama ta kasar ta Moroko. Man ya zama wata hanya da matan karkara suke dogaro da kai, ta yadda suke yinshi daga ‘ya’yan itace ta hanyoyi na gargajiya.

Bishiyar ta argan wadda ake samu a yankunan hamada na, Agadir, da Essaouira, da Tafraout, da Taroudant na Moroko, na jure wa zafi da fari, kuma tana iya rayuwa tsawon shekara 150 zuwa 200.

A dai kasar ta Moroko ana samun bishiyoyin dabino a yankuna irin su Goulmima, da Zagora, da kuma kwarin Draa, inda bishiyoyin ke yi saboda zafi da kuma kasar yankunan. Dabino na da muhimmanci a rayuwar yau da kullum a Moroko, a fannin abinci da kuma al’ada.

Ana noman dabino, wanda ke da muhimmanci na al’ada da kuma addini, a Moroko tun shekaru dubbai. A lokacin azumin Ramadan, dabino na da muhimmanci sosai a kasar da ma sauran kasashen Musulmi, inda ake buda-baki da shi da ruwa, kamar yadda Sunnar Annabi Muhammad (SAW) ta tanada.

Dabino na daga cikin kayan amfanin gona a ciki da wajen kasar, kasancewar Moroko na fitar da shi waje. Har ila yau, ba ta yadda za ka yi magana a kan Moroko ba tare da ka ambato fitaccen shayinta ba – na na’ana. Shayi ne da za ka gani kusan a koda yaushe a ko’ina, wanda ya zama wata alama ta kasa, da kuma zama wata hanya ta kyautata wa da al’ummar ta Moroko ke yi wa bakinsu.

Ana amfani da wannan shayi wajen bude taruka na tattaunawa ta abokan ciniki ko iyalai ko kuma kammala cin abinci na ciyayyar iyali. Ba a dai san lokacin da aka fara wannan ala’ada ta shayin ba a Moroko, amma an yi amanna ta soma ne daga karni na 17 a zamanin mulkin Sultan Moulay Ismail, a lokacin da ake bayar da sha’ayi a matsayin wata kyauta ta diflomasiyya ga Turawan Ingilishi.

A yau Moroko ta kasance daya daga cikin manyan kasashen da suka fi sayen ganyen shayi a duniya, musamman na China (koren ganyen shayi).

Kasuwannin dare na Marrakech ba ba wurare ba ne kawai na yawo ko shakatawa – wasu kafafe ne na tattalin ariki da kuma alama ta al’ada ta Moroko. Da da dare ya yi birnin Marrakech na juyewa ya zama wani fili mai ban sha’awa, inda kasuwannin dare musamman wadda take dandalin Jema’a el-Fna inda suke zama wata cibiya ta rayuwar birni.

Masu ziyara daga ko’ina a duniya na tururuwa zuwa wadannan kasuwanni na dare, domin sayen kayayyaki da kuma kashe kwarkwatar idanuwansu. Birnin Ouarzazate, karamin gari ne da ke yankin kudu maso gabashin Moroko, a daidai inda hamadar Sahara ta fara. Tsawon gomman shekaru wannan yankin ya kasance cibiyar hada fina-finai ta Atlas Studios, wadda tana daya daga cikin manyan wuraren yin fina-finai a duniya bayan

Hollywood da ke Amurka.

Hakan ya sa wajen ya zama wajen da ake yin fitattun fina-finai da shirye-shirye na talabijin. An yi fina-finai irin su Gladiator da Lawrence of Arabia da Kundun da kuma The Mummy har ma irin su Game of Thrones.

Tun bayan da ya hau gadon sarauta a 1999, Sarki Mohammed na shida ya mayar da kwallon kafa wata hanya ta ciyar da kasar gaba da fitar da ita a idon duniya ta zama mai tasiri, ta hanyar samar da kayayyaki da wuraren wasan na zamani da masu koyarwa kwararru da kuma bunkasa wasan har na mata.

Wannan mataki ya samar da kyakkyawan sakamako, kamar nasara mai tarihi ta tawagar Morokon inda ta je wasan kusa da karshe na gasar cin Kofin Duniya ta 2022, da komawar kasar mataki na 14 a tsakanin kasashen duniya a jadawalin kwarewa na Fifa, da kuma nasarar kasar a gasar cin Kofin Duniya ta ‘yan kasa da shekara 20 inda ta doke Argentina 2-0 ta ci kofin.

Yanzu Moroko na zama wata tauraruwa a wasan kwallon kafa a duniya, inda za ta karbi bakuncin wasan cin Kofin Afirka na bana – 2025, sannan za ta karbi bakuncin hadin gwiwa na gasar Kofin Duniya na 2030, tare da Sifaniya da Portugal.

Dan wasan Paris St Germain, Achraf Hakimi dan kasar ta Morocco, shi ne wanda aka zaba a matsayin wanda ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na Afirka na 2025, mai tsaron baya da ya lashe kyautar karon farko bayan shekara 52.

Mai tsaron bayan ya karbi kyautar sakamakon nasarorin da ya samu a 2025 tare da Paris St Geramin ciki har da lashe Champions League da Ligue 1 da Coupe de France da kuma UEFA Super Cup.

Shi ne na farko daga Moroko da ya karbi kyautar tun bayan Mustapha Hadji a shekarar 1998, kuma mai tsaron baya na farko tun bayan dan kasar Zaire, Bwanga Tshimen a 1973.

Moroko ce ta lashe yawancin kyautukan da aka raba daga ciki har da ta mace mafi kwazo a 2025 ga Ghizlane Chebbak mai buga wasa a Saudiya da mai tsaron ragar Al-Hilal, Yassine Bounou a matakin mafi taka rawar gani a shekarar nan.

Ghizlane Chebbak ta kafa tarihi a matsayin ‘yar Moroko ta farko da ta lashe wannan kyauta tun da aka fara bayar da ita a shekarar 2001. ‘Yar wasan mai shekara 35 ita ce ta zama wadda ta fi zura kwallo a raga a gasar cin kofin kwallon kafa ta Afirka ta 2024, inda ta zura kwallo mai kayatarwa a wasan karshe na gasar.

Wadanda Suka Lashe Kyautuka

Gwarzon dan kwallo Afirka: 

Achraf Hakimi (Paris St-Germain da Morocco)

 

Gwarzuwar ‘yar kwallon Afirka: 

Ghizlaine Chebbak (Al-Hilal da Morocco)

 

Mai tsaron raga na maza: 

Yassine Bonou (Al-Hilal da Morocco)

 

Matashin dan kwallo mafi kwazo: 

Othmane Maamma (Watford da Morocco)

 

Matashiyar ‘yar wasa mafi kwazo: 

Doha El Madani (AS FAR da Morocco)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco
Wasanni

Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

December 21, 2025
Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey
Wasanni

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025
‘Yan Wasa Biyar Da Tauraruwarsu Za Ta Haska A AFCON
Wasanni

‘Yan Wasa Biyar Da Tauraruwarsu Za Ta Haska A AFCON

December 20, 2025
Next Post
Wang Yi Ya Gana Da Mai Ba Da Shawara Kan Tsaron Kasa Na Firaministan Burtaniya Powell

Wang Yi Ya Gana Da Mai Ba Da Shawara Kan Tsaron Kasa Na Firaministan Burtaniya Powell

LABARAI MASU NASABA

Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

December 21, 2025
Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

December 21, 2025
An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

December 21, 2025
Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

December 21, 2025
Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

December 21, 2025
Tinubu

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025
Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

December 21, 2025
Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

December 21, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.