Domin mayar da martani game da katobarar da Firministar kasar Japan Sanae Takaichi ta yi a baya-bayan nan kan yankin Taiwan na kasar Sin da kuma rashin nuna nadamarta, jama’ar kasar Japan sun sake yin wata babbar zanga-zanga a Tokyo da yammacin jiya Jumma’a, suna neman Takaichi ta janye kalamanta.
Daruruwan mutane sun sake taruwa a gaban gidan Firaministar bayan zanga-zangar da aka yi a ranakun 21 da 25 ga watan Nuwamba. Masu zanga-zangar suna dauke da allunan da ke cewa “Takaichi ta yi murabus” da kuma “Kada ku manta da tarihi, kada ku sake maimaita irin wadannan kura-kurai,” inda suke neman Takaichi ta janye kalamanta kan yankin Taiwan na kasar Sin.
A wani taron majalisar dokokin kasar da ya gudana a ranar 7 ga watan Nuwamba, Takaichi ta yi ikirarin cewa “amfani da karfi a kan yankin Taiwan” daga babban yankin kasar Sin na iya zama “wani yanayi mai barazana ga dorewar” Japan, kuma hakan na nuna yiwuwar shiga tsakani ko kai dauki ta hanyar amfani da makamai a mashigin tekun Taiwan, wanda nan take lamarin ya jawo suka mai tsanani a cikin gidan kasar. (Abdulrazaq Yahuza Jere)














