Shugabannin jam’iyyu biyu mafi girma a Nijeriya, PDP da APC, sun kai ziyara Bauchi domin miƙa ta’aziyyarsu kan rasuwar fitaccen malamin Ɗarikar Tijjaniya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi. Tawagar PDP ƙarƙashin jagorancin Barista Kabiru Tanimu Turaki, SAN, ta isa fadar Gwamna Bala Mohammed inda suka miƙa saƙon gaisuwa ga iyalan marigayin tare da roƙon Allah Ya jikansa, Ya kuma sanya shi cikin Aljannatul Firdausi.
Barista Turaki ya bayyana Sheikh Dahiru Bauchi a matsayin ginshiƙi a fagen ilimi da tarbiyya, sannan ya tallafa da naira miliyan hamsin domin taimaka wa iyalan marigayin da wannan rashi ya shafa. Ya ce rayuwar marigayin ta kasance tsantsar hidima ga addini da ƙasa, abin koyi ga sauran malamai da mabiyan Ɗarika.
- Sarkin Musulmi Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi
- Yanzu-yanzu: Sultan, Tinubu, Kwankwaso Sun Kawo Ta’aziyyar Rasuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi
A nata ɓangaren, tawagar APC ƙarƙashin jagorancin Farfesa Nentaweh Yilwatda ta bayyana rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi a matsayin babban rashi ga al’ummar musulmi a Nijeriya da ma duniya. Farfesan ya ce Sheikh Dahiru ya yi fice wajen yaɗa dalilai na zaman lafiya, da ɗa’a da ilimi, lamarin da ya sa girmamawarsa ta zarce iyakokin ƙasa. Manyan jami’an gwamnati da sanatoci da dama sun halarci ziyarar ta’aziyyar, ciki har da Janar Aliyu Gusau (Rtd.), Sule Lamido, da Sanata Abdul Ningi.
Gwamna Bala Mohammed ya gode wa tawagogin jam’iyyun bisa wannan ziyara, yana mai cewa marigayin ya bar babban giɓi a fagen addini da tarbiyyar al’umma. Ya yi addu’ar Allah Ya jiƙan Sheikh Dahiru Bauchi da rahamarsa, Ya kuma karɓe shi cikin Aljannatul Firdausi, yana mai kira ga al’umma da su ci gaba da bin koyarwarsa ta zaman lafiya da haɗin kai.














