A wata hira da aka yi da Farfesa Idris M. Bugaje shugaban hukumar Ilmin Kimiya da Fasaha ta kasa a gidan rediyon Rhythm FM, Abuja ya bayyana cewa ilmin jami’o’in Nijeriya da ya zama ba banbanci da ilmin makaratun firamari badan gwagwarmaya da jan tunga da kungiyoyin malaman makarantun manyan gaba da sakandire suke yi ba.
Kamar yadda kusan kowane dan Nijeriya ya sanine cewar ilmin makaratun firamari a Nijeriya musamman na gwannati ya zama tamkar mushan gizagi a wasu garuruwa inda mafi yawan dalibai a makarantu ba su da gurin zama, babu ofisoshin malamai ga kuma rashin makewayoyi masu kyau da tsafta. Duk da irin makudan kudade da gwamnatoci suke warewa a kowane mataki wannan bai hana ilmin makarantun kananan makarantun gwannati tabarbarewa ba.
Sai dai kuma masana na ganin kudadan da gwannati ke warewa bai wuce cikin cokaliba na abun da ya kamata ta kasheba wajan farfado da ilimi musamman a matakin farko a kasar nan.
Bukatar Hukumar kyautata Ilimi da kimiya da Al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya (UNESCO) shine ga kowace kasa ta ware kaso kashi 26 na kasafin kudin ta ga ilimi. Amma a Nijeriya a shekarara ta 2021 kaso biyar zuwa shida aka ba bangaran ilimi, hakazalika a shekarata 2022 da ake ganin ya kamata a ma ilimi rikon dan amaryar, ilimi ya sami kashi 14 cikin darine dan farfado da ilimin bayan irin jibgar da annobar Cuta mai Shake Numfashi (Corona Birus) ta yi ma ilimin a kafatanin fadin duniya.
Ilimi baya tafiya yadda ya kamata har sai malamai sun sami kulawa amma a kasarin malaman Nijeriya cikin tsaka mai wuya suke inda su kan kasance a tsakiyar kura da siyaki.
Wasu malamai ko a jami’o’i ba su da ofisoshin da za su zauna su gudanar da ayyukan su haka tashin gwauron zabi da rayuwa ta yi ta jefa malamai da yawa cikin ni’yasun kuncin rayuwa duk da irin kokarin su na tabbatar da sun bayar da ilimi kamar yadda ya kamata wajan sauke nauyin da aka daura masu.
Kamar dai yadda aka sanine cewar ilmi shine gishirin rayuwar da yake saka rayuwa dadi, badan malamai ba da rayuwa ta kara muni da kunci. Ilmi shi yake taimakon kowane dan’adam ya gina rayuwar sa har ya haskama wasu fitila domin shi kan sa ilimi kan samar da aiki ga dunbin al’ummar kasa, sai dai wani kuskure da yake karama kwabar Nijeriya ruwa a bangaran ilimi shine wuce makadi da rawa da ake yi wajan yawaitar jami’o’i a Nijeriya fiye da makarantun kimiya da fasahohi wadanda manufar su shine koyar da sana’o’in hannu a zahiri.
Farfesa Idris M. Bugaje yana da tunani da yakini na cewar idan makaratun kimiya da fasaha suka fi yawa kuma aka inganta su a kasar nan za a sami raguwar fitintunun da sukama kasar nan daurin daimon minti haka kuma ayyuka za su wadatu a kasar nan har jama’ar kasar su fantsama cikin duniya domin fafutukar neman halaliyar su a wasu kasashe cikin kima da kulawa.
A Nijeriya, kiyasi ya nuna cewar akwai makarantun kimiya da fasaha guda 69 a inda ake da kimanin jami’o’i guda 170 abun da ake gani wannan shine barin reshe a Kama ganye.
A cewar Farfesa Bugaje kwalejojin kimiya Da fasaha suna da kaifi biyune wajan ciccida kasa ga tudun muntsira baya ga horar da dalibai ilmi akwai kuma horo da sukan iya ba ‘yan kasuwa masu aikin hannu dan samun takaddun shaidu da za su iya aiki da su a ko’ina a fadin duniya koda kuwama ba su taba shiga aji ba. Haka kuma a ka’ida daliban makarantun kimiya da fasaha ya kamata su fi yawa dan kuwa a duk karkashin wani shugaba a gurin aiki da ake bukata a ma’aikata ko gurin aiki ana bukatar masu tallafawa guda biyar wadanda suka sami horo daga kwalejojin kimiya da fasaha.
Ko shakka babu ilimin kimiya da fasaha shine zai iya tsayar da Nijeriya akan bigiran kasashen duniya wadanda suka tsaya da dugadugin su amma samuwar haka kan iya tabbatuwane kadai idan gwannati ta bayar da fifiko da kulawa ga makarantun kimiya da fasaha a kasar nan dan tabbatar da Nijeriya kasar da zata dinga cin gashin kanta ba a matsayar saniyar tatsa ba.
Hukumar Kula da Makarantun Kimiya da Fasaha ta Nijeriya, NBTE ita ce madogara a daidai wannan lokaci da Nijeriya take kokarin samun mafuta ga matsalolin da suka mata katutu da makoko.
Kamar yadda masanan ilmi da addini suka tabbatar cewar tsaro baya samuwa a tsakanin al’ummar da yunwa take ci kamar wutar daji. A daidai kuma lokaci irin wannan da Nijeriya take kukan targade da karaya gwannati ba zata iya sharema jama’a hawaye ba har sai kowa ya mike dan yakar talaucin da yake bude da baki kamar zaki. Koyan sana’a yana da kyau amma zuwa makarantar da zata ba da shaidar koyan aiki shine mafi a’ala.
Fasalin manhajar karatun makarantun kimiya da fasaha shine yake bayar da sa’ar baro tsuntsu biyu da dutse; daya, tun mutun yana dalibi yakan iya fara cin moriyar karatun sa kafin kammalawa in kuwa ya kammala ya samu takadda yakan iya samun aiki.
Damar da NBTE take da shi na horar da masu sana’o’in hannu da bayar da shaida abune da zai tsayar da kasar nan akan turbar mun tsira ga masu sha’awar kara daukaka kan su a sana’o’in su domin kuwa a dukkanin kowace sana’a buncike shi yake kara daukaka a kanta.
Da iyaye da dalibai za su gane, makarantun kimiya da fasaha ya kamata su runguma domin cigar da kasar nan gaba da kuma samun dogaro da kai domin dai bukatar maje haji sallah.
Sai dai kuma dan rungumar wannan kudiri sai fa gwannati ta gane muhimmanci da alherin da ke ciki tumbul tartare da makarantun kimiya da fasaha wajan gina kasa da gina al’umma. Haka samar da kayan koyan karatun da horarwa za su taimaka gaya wajan fardodo da kimar makarantun kimiya da fasaha a Nijeriya sannan da so samune daliban makarantun kimiya da fasaha in basu zama wadanda za su dunga amsar albashi mafi tsoka ba to su zama daidai da dukkanin daliban jami’o’i a kowane fanni ko shakka wannan ne zai kara kima da martabar makarantun kimiya da fasaha a Nijeriya.
Auwal Ahmed
Malami ne a Kwalejin Kimiya Da Fasaha Ta Kaduna A Sashen Koyar Da Aikin Jarida