Gwamnan jihar Kebbi, Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya amince da rusa majalisar zartarwa watau kwamishinonin ta jihar Kebbi daga ranar Laraba 7 ga Satumba, 2022.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren gwamnatin jihar, Babale Umar Yauri da aka rabawa manema labarai a Birnin Kebbi.
Gwamnan Jihar yana godiya kwarai da irin gudumawar da kowane memba na majalisar zartarwa ya bayar tare da gode musu bisa jajircewarsu wajen ganin sun tabbatar da zaman lafiya da ci gaban jihar a tsawon lokacin da suke kan mukamansu.
Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya kuma yabawa daukacin ‘yan majalisar da aka rusa bisa yadda suka gudanar da ayyukansu yayin da nan ba da jimawa ba za a sanar da sabuwar majalisar zartarwa ta jihar, inji takardar.
Sanarwar ta nuna cewa za a iya sake nada wasu daga cikin mambobin majalisar da aka rusa da kuma wasu daga waje.