Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a dukkanin faɗin wannan ƙasa, a ranar Laraba 26 ga Nuwamban 2025. Inda ya umarci sojoji, ƴansanda da sauran jami’an leƙen asiri da su gaggauta faɗaɗa ɗaukar ma’aikata tare da tura dubban ƙarin ma’aikatan, domin daƙile matsalolin tsaron da ƙasar ke fuskanta.
Shugaban ya kuma buƙaci majalisar dokokin ƙasar, ta fara aiwatar da aikin tabbatar da ƴansandan jihohi, domin magance yawaitar matsalar garkuwa da mutane da hare-haren ta’addanci a dukkanin faɗin ƙasar nan.
- Me Ya Fi Ci Wa Samari Da ‘Yan Mata Tuwo A Kwarya Game Da ‘Ramadan Basket’?
- Yadda Bola Ta Mamaye Sassan Babban Birnin Tarayya
Har ila yau, wasu sanatoci da ƴan majalisar wakilai, sun soki gwamnatin tarayya kan tattaunawa da ƴan bindiga, domin sako mutanen da aka kama a wasu hare-hare a Jihohin Kwara da Kebbi.
Ƴan majalisar sun buƙaci a dakatar da tattaunawa da ƴan ta’addan tare da hukunta jami’in da ya bayar da umarnin janye sojoji daga makarantar sakandaren mata ta gwamnati da ke Maga a Jihar Kebbi, inda aka yi garkuwa da ɗalibai 24 a ranar 17 ga watan Nuwamban wannan shekara.
A baya-bayan nan, sace-sacen ɗaliban dai, ya yi sanadiyar rufe makarantu da dama a Jihohin Kebbi, Bauchi, Yobe, Adamawa, Taraba, Filato, Neja, Katsina da kuma Kwara.
Gwamnatin tarayya ta kuma bayar da umarnin rufe kwalejojin haɗin kan gwamnatin tarayya guda 41 a faɗin ƙasar nan.
Kazalika, fadar shugaban ƙasar ta kare batun tattaunawa da ƴan bindigar da aka yi, inda ta ce; an yi hakan ne domin tabbatar da tsaron lafiyar waɗanda abin ya shafa.
Mai bai wa shugaban ƙasa shawara na musamman kan yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya yi watsi da raɗe-raɗin cewa; an biya kuɗin fansa, domin a sako mutanen da aka yi garkuwa da su.
Ya ce, jami’an tsaro sun yanke shawarar cewa; ba za su kai wa ƴan bindigar hari a maɓoyarsu ba, saboda ana amfani da waɗanda aka sace a matsayin garkuwa.
“Abin da wani lokaci ya kan hana su bin su shi ne, haɗarin da ke tattare da lalata da su, suna yin garkuwa da mutanenmu, kuma suna amfani da su a matsayin garkuwa, don kada a kai musu hari.
“Don haka, ba wai kawai suna son kai musu hari ba ne, suna buƙatar tabbatar da cewa; ba sa amfani da mutanenmu a matsayin garkuwa,” in ji shi.
Har wa yau, duk da ci gaba da ake yi da yunƙurin nemo ɗalibai da malaman da aka sace a Jihar Neja da kuma ayyana dokar ta-ɓaci a kan matsalar tsaro da shugaban ƙasar, Bola Tinubu ya yi, masu ɗauke da makamai na ci gaba da sace-sacen al’umma a yankuna da dama na Arewacin Nijeriya.
Wani hari da aka kai a Jihar Sakkwato ya yi sanadiyyar sace mutane aƙalla 10, ciki har da amarya da ƙawayenta, yayin da aka kai wani harin a Jihar Kogi, inda aka sace wani fasto da matarsa.
Haka nan, hukumar shige da fice ta Nijeriya ta sanar da cewa; wasu mahara sun kashe jami’anta uku a wani hari da suka kai a wajen bincike na Bakin Ruwa da ke Jihar Katsina.
Mai magana da yawun hukumar, A.S Akinlabi ta ce, lamarin ya faru ne a ranar 27 ga watan Nuwamba da dare.
Kazalika, duk waɗannan hare-hare da kashe-kashe da kuma garkuwa da mutane na zuwa ne yayin da ƙasar ke fuskantar matsi bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya yi zargin ana yi wa mabiya addinin Kirista kisan gilla a ƙasar.
Donald Trump ya sha alwashin cewa, gwamnatinsa za ta ɗauki mataki a kan Nijeriya matuƙar ba ta ɗauki matakan hana kashe kirista ba, ciki har da matakin soji.
Sai dai, gwamnatin Nijeriya ta tura tawaga mai ƙarfi zuwa ƙasar ta Amurka, ƙarƙashin jagorancin mai bai wa shugaban ƙasar shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu, inda tawagar ta gana da masu ruwa da tsaki, domin warware matsalar.
Haka nan kuma, gwamnatin Nijeriya ta musanta zargin cewa; ana yi wa kiristoci kisan gilla tare da cewa; “Matsalar tsaro ta shafi ɗaukacin al’ummar ƙasar, ba tare da la’akari da bambancin addini ba.”
Bugu da ƙari kuma, Ƙungiyar Gwamnonin Arewa (NGSF), ta jaddada goyon bayanta dangane da ƙudurin kafa rundunar ƴansandan jiha, ba tare da wani ɓata lokaci ba.
Haka zalika, gwamnonin sun amince da riƙa cire naira biliyan ɗaya ga kowace jiha, tun daga tushe, don magance matsalar rashin tsaron da ke addabar yankin.
Don haka, ƙungiyar ta ƙarfafa wa ƴan majalisar dokoki ta ƙasa da na jihohi a yankin gwiwa, da su gaggauta ɗaukar matakai; domin tabbatar da aikin ƴansandan jihohin.
Wannan ƙudiri na sama, na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar ta NGSF, Alhaji Muhammad Inuwa Yahaya ya karanta, a ƙarshen taronsu da sarakunan Arewa, wanda aka gudanar a gidan gwamnatin Sir Kashim, Kaduna, a ranar Litinin da ta gabata.
Haka zalika, taron ya kuma lura cewa; “Haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba, ya zama babban abin da ke haifar da rikice-rikicen tsaro a Arewacin Nijeriya”; don haka, ta ƙuduri aniyar bayar da shawara mai ƙarfi ga shugaban ƙasa da ya umarci Ministan ma’adanai ya dakatar da aikin haƙar ma’adanan na tsawon watan shida, domin bayar da damar tantancewa yadda ya kamata.
Haka nan, sanarwar ta ce; domin tunkarar matsalolin tsaron da ake fama da shi a Arewa yadda ya kamata, ƙungiyar gwamnonin ta kuma ƙuduri aniyar kafa wani asusun amintaccen tsaro na yankin da za a riƙa ba da gudunmuwar naira biliyan ɗaya a kowane wata daga kowace jiha da ƙananan hukumomi.
“Ƙungiyar ta kuma yaba wa gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, bisa ƙoƙari wajen ganin an sako wasu yaran da aka sace cikin gaggawa da kuma magance wasu matsalolin tsaro.
“Muna kuma yaba sadaukarwar da ma’aikatanmu ke yi a cikin kakinsu ta hanyar ci gaba da yaƙi da tashe-tashen hankula daban-daban a faɗin ƙasar nan.
Don haka, ƙungiyar ta yanke shawarar sabunta goyon bayanta ga duk wani mataki da shugaban ƙasa, kuma babban kwamandan rundunar sojin tarayyar Nijeriya zai ɗauka, na yaƙi da masu tayar da ƙayar baya zuwa yankunansu, domin kawo ƙarshen ta’addanci.
A ɓangare guda kuma, ministan tsaron Nijeriya Mohammad Badaru Abubakar, ya sauka daga muƙaminsa, yayin da ƙasar ke ci gaba da fuskantar matsalolin tsaro.
A wata sanarwa da mai bai wa shugaban Nijeriya shawara kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanguga ya fitar a ranar Litinin ya ce; Badaru ya sanar da ajiye aikin nasa ne a takardar da ya aike wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Sanarwar ta kuma ce, shugaban na Nijeriya ya amince da ajiye aikin ministan tare da gode masa kan gudumawar da ya bayar.
Haka zalika, fadar shugaban ƙasar ta fitar da sanarwar cewa; ministan ya ajiye muƙamin nasa ne, sakamakon dalilai na rashin lafiya.
Sai dai, Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya aike da sunan Janar Christopher Gwabin Musa mai ritaya majalisa dattawa, a matsayin a matsayin sabon ministan da zai maye gurbin Badaru, wanda kuma tsohon babban hafsan tsaron ƙasar nan ne.
Sanarwar ta biyo bayan murabus ɗin da tsohon Ministan Tsaro Mohammed Abubakar Badaru, ya yi ne a ranar 1 ga watan Nuwamban 2025, bisa dalilai na lafiya.
A cewar sanarwar da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ya fitar, Tinubu ya bayyana sunan Musa ga shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio. Janar Musa, mai shekaru 58, ya riƙe muƙamin babban hafsan hafsoshi daga shekarar 2023 zuwa Oktoban 2025, sannan kuma ya riƙe manyan muƙaman soja, ciki har da kwamandan ‘Operation Hadin Kai’ da kuma kwamandan rundunar sojojin Nijeriya.
Kazalika, an haife shi a Jihar Sakkwato a shekarar 1967, Musa ya shiga aikin sojan Nijeriya a 1991, ya kuma samu lambar yabo ta ‘Colin Powell Award for Soldiering a 2012’. Shugaba Tinubu ya bayyana ƙwarin gwiwa kan yadda Musa zai iya ƙarfafa ayyukan tsaron Nijeriya, yayin da yake riƙe da muƙamin minista.
Bugu da ƙari, ƙungiyar gwamnonin Arewacin Nijeriya tare da sarakunan gargajiya na yankin, sun yi wata ganawa kan matsalolin tsaron da suka addabi yankin a Jihar Kaduna.
Tun da farko dai, ƙungiyar ta yi niyyar gudanar da taron a ƙarshen makon day a gabata, amma saboda da wasu dalilai ta jinkirta zuwa ranar Litinin da ta gabata.
Gwamnonin da suka halarci taron, sun haɗa da na Jihohin Kaduna, Neja, Gwambe, Kebbi, Adamawa, Nasarawa, Jigawa, Zamfara. Yobe da sauransu.
Ƙungiyar gwamnonin Arewar, sun amince da kafa wata gidauniya, domin samar da kuɗin yaƙi da ta’addanci da kuma matsalar tsaron da ke addabar yankin.
Cikin sanarwar, gwamnonin sun bayyana cewa; sun amince kowace jiha ta bayar da naira biliyan ɗaya a kowane wata cikin asusunsu, duk da cewa; gwamnonin ba su yi cikakken bayanin yadda za su riƙa kashe waɗannan kuɗaɗe ba.
Koda-yake, dama dai masana tsaro sun jima suna bayar da shawarar yin aiki tare, tsakanin dukkanin jihohin Arewa; domin magance matsalar tsaron da gallabi yankin.
Domin kuwa, yankin na Arewacin Nijeriya ya jima yana fama da matsalar tsaro, inda ‘ɗan bindiga ke kai hare-hare kan fafaren hula tare da yin garkuwa da su ko kashe su.
Wannan mataki na gwamnonin, na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan da Shugaban Ƙasar Bola Tinubu, ya bayar da umarnin ɗaukar sabbin ‘ɗansanda, domin magance matsalolin tsaron da ƙasar ke fama da shi.
Cikin wata sanarwa da Shugaba Tinubu ya fitar a makon da ya gabata ya ce, zai duba yiwuwar amincewa da kafa ƴansandan jihohin.














