A farkon shekarar 2022, makamashin da yawansa ya kai 25% da kungiyar EU ke amfani da shi, iskar gas ne, wanda kuma rabinsa ya fito ne daga kasar Rasha.
Amma yanzu yawan iskar gas da kasashen Turai suke saya daga Rasha ya tsaya ne kan 9% kawai. A sa’i daya kuma, hauhawar farashin iskar gas da sauran makamashi na addabar Turai. A watan Agustan da ya gabata, yawan karuwar farashin makamashi a kasashe masu amfani da kudin Euro ya kai 38.3%, lamarin da ya haifar da karuwar farashin kaya.
Tsananin matsalar makamashi tana addabar kasashen Turai, amma Turawa sun gano cewa, kawarsu kasar Amurka ta nade hannu tana kallo.
Kwanan baya, Jennifer Granholm, ministar makamashin Amurka ta bukaci manyan kamfanonin tace man fetur na kasar da su dakatar da kara sayar da makamashi zuwa ketare, su mai da hankali kan kara yawan makamashi a gida cikin gajeren lokaci. Ma iya cewa, Turawa ba sa iya dogaro da taimakon Amurkawa.
Hakika dai dalilin da ya sa kasashen Turai suke fuskantar matsalar makamashi shi ne, sun bi sahun Amurka wajen sanyawa Rasha takunkumai.
Amurka ta mayar da hana Rasha sayar da makamashi, a matsayin makami, ta kuma hada hannu da kawayenta kasashen Turai. Amma Turawa sun gano cewa, lallai su kadai ne suke shan wahalar matsalar makamashi. Amurka ta nade hannu tana kallo.
Yanzu zai fi kyau ‘yan siyasar Turai su yi tunani sosai kan hanyar da kasashensu za su zabi, wadda za ta fi dacewa da moriyarsu. (Tasallah Yuan)