ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Tuesday, July 7, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Zelensky Ya Ja Hankalin Duniya Da Abubuwa Hudu Kan Yakin Ukraine

by Rabi'u Ali Indabawa
4 years ago
zelensky

A yayin da sojoji ke can fagen daga suna yaki bayan kutsen da Rasha ta yi wa Ukraine, Shugaban Ukraine din Bolodymyr Zelensky shi kuma na can yana ta ganin yadda za ya yi domin samun taimako daga kasashen duniya.

Daya daga cikin abubuwan da Mista Zelensky ya yi akwai taruka da dama da shugabannin kasashen duniya a Kyib da kuma daukar hoto da fitattun mutane.
A yayin da Ukraine ke fuskantar matsin lamba daga Rasha, Ukraine din na bukatar taimakon kasashen waje domin dakile dakarun Rasha daga ci gaba da shiga ciki.

  • Ukraine Na Bukatar Dala Biliyan Biyar Domin Yakar Rasha A Kowanne Wata

Domin samun goyon bayansa, masu kula da bangaren wasa labarai na shugaban kasar sun samo wasu hanyoyi domin jan hankalin duniya kan irin abubuwan da ake fuskanta a kasar.

ADVERTISEMENT

Taimakon muhimman mutane
Wayar da kan mutanen duniya da fitattu ko kuma sanannun mutane suke yi tun bayan fara wannan yaki, inda suke goyon bayan Ukraine tare da tara kudi masu yawa ya taimaka.

Cikin wadanda ke wannan aikin har da tsohon dan kwallo Dabid Beckham da mawaki Ed Sheeran da ‘yan fim kamar su Sean Penn da Ashton Kutcher da Mila Kunis wadda ‘yar Ukraine ce.

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Neja Ta Sanya Dokar Hana Fita Bayan Mutane 80 Sun Rasu Sakamakon Rikicin Ƙabilanci

Iran Ta Harba Wa Jiragen Ruwa Makamai Masu Linzami A Mashigar Hormuz

‘Yar fim Angelina Jolie wadda wakiliya ce ta musamman a Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta kai ziyara Ukraine a watan Afrilu inda ta hadu da masu aikin sa kai da ‘yan gudun hijira.

Mista Zellensky wanda tsohon dan wasan barkwanci ne ba wai bako bane a wannan harkar dai ya hade da mutanensa da ke goyon bayan kasarsa.

Karbar baki ‘yan siyasa
Irin wadannan hotunan Mista Zelensky yana yin su tare da shugabannin kasashen Turai inda yake neman shawo kan Tarayyar Turan da ta amince da Ukraine ta shiga kungiyar, tare da kuma samun karin makamai.

Cikin shugabannin kasashen da suka kai ziyara Kyib a ‘yan kwanakin nan har da Emmanuel Macron na Faransa da Mario Draghi na Italy da Olaf Scholz na Jamus da Klaus lohannis na Romania.

Haka kuma akwai Firaiministan Birtaniya Boris Johnson da Justin Trudeau na Canada, sai dai babu Joe Biden na Amurka.

Shugaban Amurka Joe Biden ya samar da biliyoyin daloli da kuma makamai ga Ukraine inda ya ce ba ya so ya kara jawo wa Ukraine karin wahala, musamman idan ya ce zai tsaya a kasar a tafiyar da za ya yi nan gaba zuwa Turai.

Kasashen da ba na Yamma ba sun fi samun rabuwa a goyon bayan da suke ba Ukraine a yaki, duk da cewa Mista Zelensky na ta neman taimako, inda ake jan hankalin kasashen Afrika kan abin da zai iya biyowa baya sakamakon yakin Ukraine.

Ya bayyana cewa Yan Afrika sun zama kamar fursunonin yaki kuma suna fuskantar barazanar yunwa saboda yakin ya jawo karancin taki da hatsi – sai dai an gano kasashen Afrika hudu ne kacal cikin 55 suka shiga taron inda aka yi ta intanet.

Sauran tarukan da aka yi na bidiyo an halarce su kuma an yaba wa Mista Zelensky kan bayanansa da ya yi wa Majalisar Tarayyar Amurka da Tarayyar Turai da Jamus da Japan da Faransa da Sifaniya da Majalisun Italiya da sauran su.

Nuna wa duniya barnar Rasha
Mista Zelensky ya kuma yi wani abu da ya nuna wa duniya irin barnar da Rasha ta yi wa Ukraine, ta hanyar zagayawa zuwa biranen da aka lalata da kuma kai zuyara ga sojojin da ke fagen daga da asibitoci.

Ya yi tafiyarsa ta farko zuwa birnin Kudancin kasar da yaki ya daidaita a ranar Asabar inda ya yi zagaye a birnin Mykolaib.

A lokacin da ya kai, Mista Zelensky ya je ya duba gine-ginen da suka lalace haka kuma ya hadu da sojoji da jami’ai da ma’aikatan lafiya.

Haka kuma shugaban Ukraiendin ya kai ziyara birnin Odesa da ke Yammacin kasar wanda aka yi ta kai masa harin makamai masu linzami tun bayan da aka fara wannan yaki.

A cikin ‘yan makonnin nan, ya kai ziyara wasu daga cikin biranen da ake yaki ciki har da Kharki da ke Gabashin kasar, inda ya bijirewa dakarun Rasha ya je har wurin da ake tsananin yaki.

zelensky
Rabi'u Ali Indabawa
+ postsBio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Adadin Mutanen Da Tsananin Zafi Ya Kashe A Turai Ya Haura Dubu 1,300 —WHO
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Pakistan Ta Kashe Mutum 36 A Hare-haren Da Ta Kai Kan Iyakarta Da Afghanistan
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Gwamnatin Tarayya Ta Bayyana Dalilanta Na Sake Fasalin Hukumar NYSC
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Sarkin Zazzau Ya Umarci A Soke Wasu Al’adu Da Ke Kawo Wa Aure Cikas

MASU ALAKA

Gwamnatin Neja Ta Sanya Dokar Hana Fita Bayan Mutane 80 Sun Rasu Sakamakon Rikicin Ƙabilanci
Manyan Labarai

Gwamnatin Neja Ta Sanya Dokar Hana Fita Bayan Mutane 80 Sun Rasu Sakamakon Rikicin Ƙabilanci

July 7, 2026
Iran Ta Harba Wa Jiragen Ruwa Makamai Masu Linzami A Mashigar Hormuz
Manyan Labarai

Iran Ta Harba Wa Jiragen Ruwa Makamai Masu Linzami A Mashigar Hormuz

July 7, 2026
Hukuma Ta Tilasta Wa Alƙali Yin Ritaya Saboda Karɓar Cin Hanci A Kano
Labarai

Hukuma Ta Tilasta Wa Alƙali Yin Ritaya Saboda Karɓar Cin Hanci A Kano

July 7, 2026
Next Post
Za A Kammala Babbar Hanyar Kaduna-Zariya Cikin Wata 6 Masu Zuwa — Gwamnati

Tsadar Rayuwa Da Karuwar Ta’addanci Na Ci Gaba Da Tagayyara ‘Yan Nijeriya

ADC Ta Zargi Gwamnatin Tinubu Da Jefa ‘Yan Nijeriya Miliyan 17 Cikin Yunwa

July 7, 2026
Kasuwa Ce Ke Saita Tsarin Cinikayyar Sin Da EU In Ji Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin

Kasuwa Ce Ke Saita Tsarin Cinikayyar Sin Da EU In Ji Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin

July 6, 2026
Dukkan Kabilun Kasar Sin Na Zaman Tsintsiya Madaurinki Daya

Dukkan Kabilun Kasar Sin Na Zaman Tsintsiya Madaurinki Daya

July 6, 2026
Mutane 15 Sun Mutu A Hatsarin Mota A Jihar Kwara

Mutane 15 Sun Mutu A Hatsarin Mota A Jihar Kwara

July 6, 2026
Gwamnatin Sin Ta Fara Aika Zagayen Farko Na Kayakin Agajin Gaggawa Ga Venezuela

Gwamnatin Sin Ta Fara Aika Zagayen Farko Na Kayakin Agajin Gaggawa Ga Venezuela

July 6, 2026
FIFA Ta Tsallake Iyakarta Dangane Da Batun Dakatarwar Balogun – UEFA

FIFA Ta Tsallake Iyakarta Dangane Da Batun Dakatarwar Balogun – UEFA

July 6, 2026
Shugabannin Sin Da Madagascar Sun Yi Musayar Sakon Taya Murnar Cika Shekaru 20 Da Kulla Alakar Diflomasiyya Tsakaninsu

Shugabannin Sin Da Montenegro Sun Yi Musayar Sakon Taya Murnar Cika Shekaru 20 Da Kulla Alakar Diflomasiyya Tsakaninsu

July 7, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.