Nan gaba kadan kasar Sin za ta kaddamar da katafariyar masana’antar kera taurarin dan’adam mafi girma a nahiyar Asiya, wadda za ta rika samar da taurarin dan’adam har 1,000 a duk shekara. Masana’antar dake yankin raya harkokin sufurin sama na birnin Wenchang ko WIAC, a lardin Hainan na kudancin kasar Sin, za ta samar da zarafi na harba taurarin dan’adam nan take bayan kammala kirarsu daga sansanin harhadawa.
Karkashin yankin masana’antar, kamfanoni sama da 20 masu gudanar da ayyukan farko-farko na harhada kumbunan da na karshen kammala su, sun daddale yarjeniyoyin kasancewa tare a yankin, matakin da zai kara bunkasa cikakken yanayin aiwatar da matakan gina rokoki, da taurarin dan’adam, da harba su da kuma tantance su.
Har ila yau, babbar masana’antar na kunshe da cibiyar kasa da kasa ta kera taurarin dan’adam ta zamani, da cibiyar kasa da kasa ta bincike da samar da kayayyaki masu nasaba da taurarin dan’adam da rokoki.
Bugu da kari, ta kunshi wata babbar masana’anta, da cibiyar gwaji da sanya ido, da kananan cibiyoyin samar da muhimman kayayyaki guda takwas. Masana’antar ta Sin za ta zamo irinta daya tilo da za ta rika gudanar da ayyukan harhada taurarin dan’adam da kuma aikin sanya su cikin kwanson roka domin harbawa. (Saminu Alhassan)














