Wani rahoto game da binciken harkokin zuba jari a ketare da ake wallafawa a jaridar Financial Times ta Birtaniya ya nuna Sin a matsayin kasar da mafi yawan masana a fadin duniya ke ganin za ta fi kara zuba jarin kai tsaye a ketare a 2026.
Rahoton da aka fitar ranar Alhamis ya kuma nuna cewa karfin hada-hadar cinikayya da zuba jari na karkata cikin sauri zuwa ga kasashe masu tasowa, inda kasashen ke zaman masu ingiza ci gaban tattalin arzikin duniya.
Rahoton ya nazarci manyan masana 101 na duniya kan harkokin zuba jari kai tsaye a kasahen waje a watan Oktoban 2025. Kuma da aka nemi su bayyana wurare 3 da ake hasashen za su fadada jarinsu a ketare a 2026, an samu adadi mafi yawa na ambaton kasar Sin inda jimilar ta kai 74. (Mai fassara: FMM)














