Rahotanni sun ce ‘yan bindiga sun sako wasu masallata 43 da suka yi garkuwa da su a ranar Juma’ar da ta gabata a wani babban masallaci da ke unguwar Zugu a karamar hukumar Bukkuyum a Jihar Zamfara.
Leadership Hausa ta gano cewa tun da farko masu garkuwar sun karbi Naira miliyan biyar domin a sako su bayan sun kwashe kwanaki suna tattaunawa.
- Matar aure ta bukaci kotu ta raba aurenta da mijinta saboda yawan jima’i
- Wadanda Suka Kware Wajen Rashawa Ba Za Su Iya Kawo Karshenta Ba – Hakeem Baba Ahmed
“Daya daga cikin wadanda aka kama ya mutu a hannun wadanda suka yi garkuwa da su. Masallatan da aka sace, an ajiye su ne a wani tsauni tsakanin wani yanki da aka fi sani da Marina da wani katafaren daji mai ban tsoro da ake kira Barikin Daji a karamar hukumar Gummi ta jihar,” kamae yadda wata majiya ta bayyana.
“An yi musu aiki ta jiki ba tare da hutu ko abinci ba. Wasu daga cikinsu ba za su iya zama ko tsayawa ko magana ba,” a cewar majiyar.
An tattaro cewa bayan an biya kudin fansa ‘yan bindigar sun bukaci ‘yan uwan wadanda aka sace a dajin Barikin Daji su dauko wadanda suka kashe.
Wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce, “Bayan haka al’umma sun hada kai suka aika da mahaya babura da dama zuwa dajin kuma an fitar da su daga daji da yawa saboda yawansu.
“An kai su gefen babbar hanyar Daki Takwas-Zuru inda motoci suka dauke su zuwa unguwarsu.”
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Muhammad Shehu, ba a samu damar jin ta bakinsa ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.