Assalamu Alaikum! Barkanmu da sake kasancewa da ku a cikin wannnan shiri wanda muke zabo batu (Topic) duk mako dan tattaunawa a kansu. A wannan makon za mu tattauna ne a kan KURAKUREN IYAYE YAYIN TARBIYYA. Tabas! Sau tari musamman a irin zamanin da muke ciki iyaye na sakaci sosai wajen tsayawa gun ba ‘ya’yayensu tarbiya, kama daga kan Uba zuwa kan Uwa.
Sakacin Iyaye Maza: A wannan zamanin Maza da yawa za ka iya samu ba su san me ake a gidansu ba musamman ‘ya’yayensu. Gaba daya za ka tarar ya sake ma Mace tarbiyar da kulawa da yaran, wani idan ya sa kai ya fice tun safe ba za ka kuma ganinsa ba sai dare, lokacin za ka iya tararwa yaran sun yi bacci, idan ma idonsu biyu shi din ya gaji bai da lokacin da zai zauna ya kula da abin da ke tafiya a cikin gidansa ko da na mintuna ne kuwa. Abin da suka sani shine idan yaro ya yi mara kyau su danganta da uwa da rashin zamansu sun manta da kiwo ne Allah ya dora a wuyansu.
Mace ce ginshikin tarbiyar yara wanda shi ya sa ake cewa idan za ka yi Aure ka auro ma ‘ya’yayenka Uwa tagari, sai dai hakan ba yana nufin ka sake ma mace ragamar komai na tarbiya ba ne dole tana bukatar mataimaki musamman yaranmu na zamani masu zuwa da wayau sosai dole sai iyaye biyu sun yi tsayuwar daka gun kulawa. An sani Namiji shi ke fita gwagwarmaya wajen nema domin iyalansa. Sai dai yana da kyau har ila yau a ce ya ware lokuta na musamman wajen kulawa da su idan ba haka ba, zai gama neman kudinsa bayan shekaru ya tsinci yaransa wasu iri ba yadda ya so ba, ma’ana tarbiyar ta lalace ko wani abu wanda ba zai taba jindadin hakan ba. Wannan kenan. A cikin al’kur’ani maigirma Suratul Attahrim Aya ta 6. Allah (SWT) yana cewa, “yaku wadanda kukayi Imani! Ku kare kanku da iyalanku daga wuta makamashinta mutane da duwatsu ne. A kanta akwai wasu mala’iku masu kauri, masu karfi. Ba su saba wa Allah ga abin da ya umarce su, kuma suna abin da ake umarninsu”. Allah yaba mu ikon kulawa Ameen.
Sakacin Iyaye Mata: wajibi ne duk Uwa tagari ta yi wa yaranta tarbiyya tagari dan su zamanto na gari. Tarbiya ita ce gatan da iyaye za su iya ma ‘ya’yansu wanda zai zama tsaninsu kan addini da zamantakewa cikin al’umma. Zamani Allah ya kawo mu inda za ka tarar waya da ‘social media’ ya fi ma wata Uwar yaranta, wata ko me yaron yake ba ruwanta, haka a kan waya ma wata sai ta kora yaran da cewan sun dame ta ba ruwanta da matsalar yaran ko da a makaranta an musu wani abun zai yiwu ‘information (bayani)’ ne me ma’ana ya kawo ta kore shi. Yau da gobe da na zuwa ana korar shi har zai gaji ya daina kokarin kawo wa uwar lalurarsa ko da ana mishi wani mugun abun da ya kamata ta ankara tun da ba maida hankali ta yi wajen lura da su ba bare ya dame ta, abin da ta sani kawai ta dafa ta ba su su ci shikenan. Wata ko wankansu da tsafta ba ruwansa ba ta gyara kanta ba 24/7 tana ‘social media’ bare ta gyara su.
Ire-iren haka ne sai kaji ana ta bata yarinya ko yaro tsawon lokaci in ba abin ya yi tsamari ko ya zo da matsala ba, ba a taba sani ko ka ji an sani a lokacin da bakin alkalami ya bushe, ma’ana lokaci ya kure. In ka zo bangaren yara mata za ka samu wasu Matan sai ka ga ‘yar yarinya ta yi ‘toilet’ tana ta magana “na gama” kuma ita ba ta kai wanke ma kanta ba amma sai ka samu wannan uwar na zaune, abun ba zai ba ka mamaki ba sai ta soma kiran yayyun wannan yarinyar tata maza su wanke mata, wani ma kila dan dan’uwan ne ko kanin ita wannan uwar ko dan uwan uban. Kai wani lokaci ma sai dai Uban ya fita da kansa ya yi wannan aikin.