Jam’iyyar APC a jihar Zamfara ta yi watsi da zargin da ke alaƙanta ƙaramin Ministan tsaro, Bello Mohammed Matawalle, da aiyukan ƴan bindiga, tana mai cewa zargin makirci ne na siyasa domin ɓata masa suna.
A wata sanarwa da Sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar a jihar, Yusuf Idris Gusau, ya fitar, APC ta ce jagororin ƴan bindiga da dama, ciki har da Bello Turji, sun fito fili a bidiyo suna musanta duk wata alaƙa da Matawalle, ko a lokacin da yake gwamna ko a yanzu a matsayin minista.
- Wata Ƙungiya Ta Fara Bin Digdigin Takardun Karatun Matawalle
- Zuwan Tsoffin ’Yan Wasan Barcelona Abuja Ya Nuna Ana Samun Zaman Lafiya A Nijeriya – Matawalle
Jam’iyyar ta zargi gwamnatin jihar Zamfara ƙarƙashin Gwamna Dauda Lawal da ƙoƙarin ƙirƙirar labaran ƙarya da kuma amfani da gwamnati wajen ɗaukar mutane da ƙungiyoyi domin matsa lamba a cire Matawalle daga muƙaminsa. APC ta kuma yi kira ga hukumomin tsaro da na shari’a su binciki zargin sakin wani ɗa bindiga Musa Kamarawa, duk da kasancewar shari’arsa na gudana a kotu.
APC ta jaddada cewa Matawalle ya bi dukkan matakan tantancewa kafin naɗa shi minista, tare da tunatar da irin matakan sulhu da gwamnatinsa ta ɗauka a baya wanda jam’iyyar ke cewa sun taimaka wajen rage matsalar tsaro a wasu sassan jihar. Jam’iyyar ta buƙaci jama’a su yi watsi da abin da ta kira zarge-zargen siyasa marasa tushe.














