A ranar 11 ga watan Oktoba 2020 mun yi sharhi a kan takaddamar da ke tsakanin Rundunar ‘Yansanda da Hukumar Kula da Aikin ‘Yansanda a kan shirin daukar sabbin ‘yansanda don fuskantar matsalolin tsaro a kasar nan.
A wannan karon Hukumar Kula da Aikin ‘Yansanda ta sanar da shirin fara daukar sabbin Kuratan sai Rundunar ‘Yansanda ta sana da cewa, al’umma su yi watsi da sanarwar.
- Da Dumi-Dumi: Jami’an Tsaro Sun Kai Samame Gidan Tukur Mamu
- Chelsea Ta Nada Potter A Matsayin Sabon Kocinta
Duk da Hukumar Kula da Aikin “Yansanda ta dakatar da shirin daukar Kuratan, amma hakan yana nuna cewa, har yanzu takaddamar da ke tsakanin Rundunar ‘Yansanda da Hukumar Kula da Aikin ‘Yansanda yana bai kare ba.
A kan haka mjka sake kawo muku sharkin da muka yi a waccan lokacin don gargadi a kan matsalar da takaddamar ka iya haifarwa ga bangaren tsaron kasar nan.
Yayin da ake fuskantar matsalar tsaro a sassan Nijeriya, wanda hakan ke haifar da kiraye-kirayen kara daukar matakin ganin an kawo karshen mastalolin gaba daya, amma sai gashi ‘yan Nijeriya sun wayi gari da takaddama a kan waye zai jagoranci daukar Kurata 1,000 aikin rundunar ‘yansandan Nijeriya.
A kwanaki ne Kwamitin mutum uku na Kotun Daukaka Kara kakrkashin jarogarancin Maishari’a Olabisi Ige ta yanke hukuncin cewa, Babban Sufeton ‘Yansanda da Rundunar ‘Yansanda basu da hurumin daukar Kruratan ‘yansanda a kasar nan.
Kotun ta zartas da cewa, Hukumar Kula da Aikin ‘Yansanda (PSC) ne kawai ke da hurumi na shari’a na daukar Kuratan ‘yansanda, a kan haka Kotun ta haramta daukar Kuratan da Rundunar ‘Yansanda ta jagoranta.
Hukumar Kula da Aikin ‘Yansandan ta maka Sufeton ‘Yansanda ne a kotu inda take kalubalantar daukar Kurata 10,000 da Rundunar ta jagoranta inda kotun ta zartas da cewa, Rundunar ‘yansanda bata da hurumin jagorantar daukar Kuratan, “Dauka, karin girma da korar ‘yansanda ba hakki ne na Rundunar ‘Yansanda ba, hakki ne na Hukumar Kula da Aikin ‘Yansanda.” In ji Kotun.
A kan haka Hukumar Kula da Aikin ‘Yansadan ta nemi kotu ta soke shirin da Rundunar ‘Yansanda ta yi na daukar Kuratan ‘yansanda a fadin kasar nan gaba daya.
Tun da farko a Mai Shari’a Inyang Ekwo na Babban Kotun Tarayya a hukuncin da ya yanke a ranar 2 ga watan Disamba 2019, ya kori karar da Hukumar Kula da Aikin ‘Yansandan ta shigar ne, abin da ya sa suka daukaka karar, inda Kotun Daukaka Kara ta zartar da hukuncin da ya yi musu dadi.
Wannan jaridar na daukar takaddamar da ke tsakanin PSC da IGP a kan wanda yake da hurumin daukar Kuratan ‘yansanda a mastayin wani babbar tarnaki ga kokarin da ake yi na kawo karshen matsalar tsaron da ake fuskanta a halin yanzu.
A ra’ayinmu bai kamata a ce hukumomin gwamnati biyu sun shiga wannan takaddamar ba musamman ganin aikin da ke a gaban sun a tabbatar da tsaron al’umma a halin yanzu.
Mun damu matuka ganin yadda ake fustantar matsalar tsaro a sassan kasar nan amma bangaren rundunar tsaronta na takaddama a kan wanda yake da hurumin jagorantar daukar Kuratan ‘Yansanda a Nijeriya, wannan takaddamar na iya kawar da hankalinsu daga kokarin da ake yi na yaki da matsalar tsaro da ‘yan bindiga a Nijeriya.
Tabbas wannan takaddama abin takaici ne, ganin muna cikin lokacin da yakamata a hada karfi da karfe a yakin da ake yi da ‘yan bindiga.
Ra’ayi ya hadu a kan cewa, Nijeriya na bukatar karin ‘yansanda, don matakin Majalisar Dinkin Duniya shi ne na dan sanda daya aka ‘yan kasa 600.
Rahoton Majalisar Dinkin Duniya na shekarar 2006 ya ayyana samar da ‘yansanda 300 ga ‘yan kasa 100,000.
An kuma lura da kasashe tara kawai suka iya samar da ‘yansanda 100 ga ‘yan kasa 100,000. Rahoton ya kara bayyana cewa, kasashen da suka fi kuka da wannan ka’ida suna yankin Asiya ta Yamma da Gabas da kuma Kudancin Turai.
A kwanan ne, Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya bayyana cewa, a jiharsa ‘yansanda 30 ke kula da kauyuka fiye da 100.
Har zuwa yau da muke maganar nan, Rundunar ‘Yansanda ba su fito sun karyata wannan bayani ba na Masari.
Ko ba komai maganar tana fitowa ne daga bakin Babban Jami’i mai kula da harkokin tsaron jihar, jihar da take fuskantar matsalolin tsaro wadda ta kai ga rasa rayuka da dukiyoyin al’umma da dama a ‘yan shekarun nan.
Ana tsananin fuskantar karancin jami’an ‘yansanda a Nijeriya, maimakon a fuskanci hanyoyin da za su kawo karshen wannan matsalar wanda hakan zai kara dawo da mutuncin rundunar sai gashi takaddamar wa zai jagoranci daukar Kurata ya turnuke kasa.
A ra’ayinmu wannan takaddamar tsakanin hukumomin biyu masu muhimmanci ga shirin tabbatar da tsaro a kasar nan yana nuna rashin sa ido ne daga gwamnati kuma yakamata a gaggauta daukar matakin warware matsalar.
Tabbas babu mai kokwanton cewa, matsalar tsaro na daga cikin manyan-manayn matsalolin da ke fuskantar kasar a wannan lokacin, saboda haka samun takaddama a tsakanin PSC da NPF abin takaici ne kwarai da gaske, musamman ganin harkokin ‘yanta’adda irinsu garkuwa da mutane, fyade da sauran ayyuykan masu aikata manyan laiffuka ya taukura a’lumma.
Muna Allah wadai da takaddamar neman girma tsakanin cibiyoyin gwamnatin guda biyu, kuma abin takaci ne ma’aikatar da ke kula da cibiyoyin biyu ta kasa samar da fahimtar juna a tsakanin su.
A kan haka muna kira da Ma’aikatar Kula Harkokin ‘Yansada ta shigo don samar da yanayin fahinta a tsakaninsu, ta haka za a samu tabbacin samar da isassun ‘yansanda don fuskantar matsalolin tsaro a fadin kasar nan.