Wakilin dindindin na kasar Sin a Majalisar Dinkin Duniya (MDD) Fu Cong, ya yi tsokaci a yayin taron muhawara na kwamitin sulhun MDD, kan batun “Karfin jagoranci don zaman lafiya”, inda ya sake gargadin kasar Japan da ta janye kalamanta na kuskure.
Fu Cong wanda ya yi kiran a jiya Litinin, ya ce yunkurin nuna karfin jagoranci don zaman lafiya, da farko yana bukatar darajanta zaman lafiya da rike adalci. Ya ce a bana ake cika shekaru 80 da cimma nasarar yakin da Sinawa suka yi da mamayar dakarun kasar Japan, da yaki na duniya na 2 na adawa da tafarkin murdiyya. A lokacin da al’ummun kasa da kasa ke bitar tarihi, da tsara makoma, firaministar kasar Japan Takaichi Sanae, ta aikata abin da bai dace ba, inta ta yi ikirarin cewa, a halin yanzu Japan na fuskantar barazanar dorewarta, wanda ke da alaka da yankin Taiwan na Sin, tana nuna alamar yin barazanar cewa, Japan za ta iya sanya hannu cikin batun Taiwan ta hanyar amfani da karfin soja.
Fu Cong ya ce wannan wani mummunan yanayi ne na tsoma baki a harkokin cikin gida na Sin, wanda ya saba wa alkawarin da Japan ta yi a matsayinta na kasar da ta sha kaye, a yakin duniya na biyu a hannun kasar Sin da sauran al’ummun kasa da kasa. Kazalika, matakin ya kalubalanci sakamakon nasarar yakin duniya na biyu, da tsarin kasa da kasa bayan yaki, ya kuma saba wa ka’idojin huldar kasa da kasa bisa tushen manufofin yarjejeniyar tsarin mulkin MDD, wanda ke haifar da babban hadari ga yunkurin kiyaye zaman lafiya a Asiya, da ma duk duniya baki daya.
Daga nan sai Fu Cong ya sake jaddada gargadin Sin ga Japan, cewa ta janye kalaman kuskure da ta furta, ta kuma yi bita da nadama, tare da dakatar da ci gaba da tafiya a kan hanya ta kuskure. (Amina Xu)














