Kotun ƙoli da Majalisar Shari’a ta Kasa (NJC) sun miƙa ta’aziyya ga iyalan tsohon Babban Alkalin Nijeriya (CJN), Mai Shari’a Ibrahim Tanko Muhammad, wanda ya rasu da sanyin safiyar Talata.
Cibiyoyin, a cikin sanarwar da suka fitar daban-daban, sun yaba wa kyawawan halayen marigayi, tsohon CJN Tanko.
A cikin wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai da Hulda da Jama’a a Kotun Koli, Dr. Festus Akande ya fitar, kotun koli ta ce, “Kotun Koli ta Nijeriya ta yi jimamin rasuwar Mai Shari’a Ibrahim Muhammad Tanko, CJN na 17 a Nijeriya, wanda ya rasu da sanyin safiyar yau, Talata, 16 ga Disamba, 2025, yana da shekaru 72.
“Wa’adin Alkali Tanko a matsayin Babban Alkalin Nijeriya daga 2019 zuwa 2022 ya kasance cike da jajircewa ga bin doka, ‘yancin kai na shari’a, da kuma gudanar da gaskiya da adalci.” In ji Kotun














