Ofishin Uwargidan Gwamnan Zamfara ya jagoranci rabon tallafin kuɗi kimanin N200,000 ga dattawa 250 domin inganta harkar kasuwancinsu.
Shirin wanda shi ne karo na uku wanda aka sanyawa suna “Remi Huminitarian Initiative’ (RHI) a ƙarkashin shirin da uwargidan shugaban ƙasa Remi Bola Tinubu ke jagoranta domin tallafawa dattawa masu karamin karfi 250 daga kowacce jiha a Nijeriya.
Tallafin na kuɗi an raba shi ne a Gusau babban birnin Jihar, ƙarkashin kulawar ofishin uwargidan gwamnan Jihar Zamfara, Huriyya Dauda Lawal, wanda aka sanya masa taken “Tabbatar da Walwala da Farin Cikin Dattawa”.
Wadanda suka ci gajiyar tallafin kuɗin a Jihar, Dattawa ne waɗanda suka haɗa da maza da mata da ke da ƙananan kasuwanci daban-daban a faɗin ƙananan hukumomi 14 na Zamfara.














